Majalisar dattawa ta bukaci Buhari da ya sanya dokar ta baci kan tsaron kasar

Majalisar dattawa ta bukaci Buhari da ya sanya dokar ta baci kan tsaron kasar

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci a fannin tsaron kasar. Hakan na daga cikin matsayar da suka yanke a zaman majalisa na ranar Laraba, 29 ga watan Janairu.

A zaman, majalisar dokokin ta tattauna sosai a kan matsalolin tsaron Najeriya inda wasu yan majalisar ke ganin sauya fasalin tsaron da ake ciki ne mafita.

Yayinda ya ke duba lamarin; Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce ba a kokarin da ya kamata a yi a Najeriya.

Sanata Abaribe ya bukaci gwamnati mai mulki da ta yi murabus, inda ya yi korafin cewa gwamnatin ba za ta iya yiwa kasar komai ba kuma.

Majalisar dattawa ta bukaci Buhari da ya sanya dokar ta baci kan tsaron kasar
Majalisar dattawa ta bukaci Buhari da ya sanya dokar ta baci kan tsaron kasar
Asali: UGC

Duk a kan lamarin tsaron, Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana cewa an ja tsarin tsaron kasar.

A cewar Sanata Omo-Agege, ya kamata kasar ta yi duba ga tsarin tsaro na jiha.

Da ya ke kai lamarin zuwa ga wani bangare na daban, Sanata Mathew Urhoghide ya ce babu daidaituwa a tsakanin hukumomin tsaron kasar.

Ya ce mai ba kasa shawara a kan tsaro ne ke shawarartar shugaban kasa kuma cewa ya kamata ya iya hada kan hukumomin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CHRSJ ta yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari game da sha’anin tsaro

Bayan tattaunawa na tsawon lokaci kan lamarin majalisar ta bukaci Shugaban kasa da ya sanya dokar ta baci kan lamarin tsaro Sannan ya kafa kwamitin wucin gadi don binciken hukumomin tsaro da kuma kawo wa majalisa rahoto.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mambobin majalisar sun yi kira ga shugabannin tsaro da su yi murabus daga kujerunsu. Hakan na daga cikin matsayar yan majalisar bayan sun yi muhawara kan lamarin tsaron kasar a zamansu na ranar Laraba, 28 ga watan Janairu a Abuja.

Wani dan majalisa, Abubakar Fulata, ya sanar da takwarorinsa a zauren majalisar cewa shugabannin tsaron sun yasar da amfaninsu.

A cewarsa, kasar za ta kasance cikin hatsari idan aka bar wadannan mutane suna cigaba da maimaita abu guda tare da sa ran samun banbancin sakamako wajen yaki da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng