Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai: APC ta sake lamunce wa Doguwa

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai: APC ta sake lamunce wa Doguwa

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Comrade Adams Oshiomhole a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ya ce kin cike gurbin Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai alamu ne da ya nuna cewa mambobin majalissar sun san cewa lallai Alhassan Doguwa zai sake dawowa majalisar.

Oshiomhole ya fai hakan ne a yayinda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sauran mambobin majalisar dokokin tarayya na APC don kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa na Asokoro da ke Abuja.

An sake zabar Doguwa a zaben da aka sake gudanarwa a ranar Asabar da ya gabata domin cigaba da wakiltan al’umman mazabar Doguwa/Tudunwada a jihar Kano.

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai: APC ta sake lamunce wa Doguwa
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai: APC ta sake lamunce wa Doguwa
Asali: Twitter

“Daga dukkan alamun da takwarorinka suka nuna, kakakin majalisar ya kasance a Kano, haka ma mataimakin Shugaban majalisar ya kasance a Kano kuma ba komai bane ya sa suka zabi kin cike gurbin ka ba illa kamar yadda mutanen mazabarka suka zabe ka, suma suna jiran a sake zabarka.

“Na yi imani cewa Allah ya baka dama na biyu. Kasancewar kaakakin majalisa a Kano ya nuna cewa ya rike ka da muhimmanci sosai. Da gangan suka ki cike gurbinka kuma kamar mu, mutanen mazabarka za su dawo da kai majalisa. Ina ganin b azan ce wani abu da ya fi wannan ba,” inji shi.

Oshiomhole, wanda ya bayyana Doguwa a matsayin dan jam’iyya na asali wanda gudunmawar da yake bayarwa a muhawarar majalisar wakilai ya amfani gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sabonta imanin APC a bangaren shari’a.

Ya yi watsi da batun cewa APC ta fara shan kasha a hannun jam’iyyar adawa saboda rikice-rikicen da ake a jam’iyyar reshen wasu jihohi, ina yace nasarar Doguwa ya nuna karbuwar APC a wajen masu zabe a jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Maryam Sanda za ta daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke mata

Gwamna Ganduje yayina ya ke jawabi da fari, ya ce sun kawo ziyarar ne domin gabatar da takarar shaidar cin zaben Doguwa da kuma bukatarsa na sake neman matsayin Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel