Akwashiki: Sanatoci ba za su bibiyi batun sace sandar girman Majalisa ba
- Sanatoci sun ce babu su babu maganar abin da aka yi a shekarar 2018
- A shekarun baya ne aka taba yin awon-gaba da sandar girman Majalisar
- Majalisar Tarayyar ta ce abin da aka yi a can ya riga ya wuce a wajen ta
Majalisar Dattawa ta yi magana a game da wani rikici da aka yi a shekarar 2018 a lokacin da Bukola Saraki ya ke shugabantar majalisar.
A cikin Watan Afrilun 2018 ne wasu ‘Yan daba su ka shigo har cikin majalisar tarayya, su ka sungume sandar da ke nuna alamun girma.
Sanatocin Najeriya sun bayyana cewa wannan abu ya riga ya wuce, kuma ba za a sake gudanar da wani bincike a game da lamarin baya ba.
Mai magana da yawun bakin Sanatoci a majalisar dattawa, Godiya Akwashiki ce ta bayyana mana wannan a cikin farkon makon nan.
Sanatar ta shaidawa ‘Yan jarida acewa duk abin da ya faru a majalisar da ta shude, ya zama tarihi, don haka ba za a sake tado da shi ba a yau.
KU KARANTA: Shugaban majalisa ya koka da halin rashin tsaro a Najeriya
Kamar yadda Jaridar This Day ta rahoto, Sanata Akwashiki, ta bayyana cewa wannan majalisar da ta ke ci a yanzu, ta fara ci ne daga 2019.
Ana zargin cewa akwai hannun Sanata Ovie Omo Agege a lokacin da aka turo ‘Yan banga su ka yi gaba da sandar girman majalisar a 2018.
Sai dai yanzu Sanatan na APC ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa a karkashin Sanata Ahmad Lawan a wannan majalisar ta tara.
Kwanakin baya kun ji cewa wata kungiya a Amurka ta zargi Omo-Agege da aikata laifi a lokacin da ya ke aiki a kasar waje a shekarun baya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng