Majalisar dattawa ta dawo sannan ta dage zamanta don jimamin mutuwar wani dan majalisar wakilai

Majalisar dattawa ta dawo sannan ta dage zamanta don jimamin mutuwar wani dan majalisar wakilai

- Majalisar dattawa ta dawo zama bayan hutun makonni biyar a ranar Talata, 28 ga watan Janairu

- Yan majalisar sun dawo zama da ganawar sirri wanda ya shafe tsawon kimanin sa’a guda, sun yi zama na dan lokaci sannan suka dage zamansu zuwa ranar Laraba

- Sun dage zaman ne domin karrama wani mamba na majalisar wakilai, Muhammadu Gawo, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Disamba

Majalisar dattawa a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ta dawo zama bayan hutun makonni biyar.

Yan majalisar sun dawo zama da ganawar sirri wanda ya shafe tsawon kimanin sa’a guda, sun yi zama na dan lokaci sannan suka dage zamansu zuwa ranar Laraba.

Bayan ganawar sirrin, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce batutuwan da aka tattauna a zaman sun kasance kan wasu tsare-tsare da yan majalisar za su yi aiki kai a 2020.

Ya ce majalisar dattawan za ta bayar da muhimmanci sosai kan magance matsalar tsaro a fadin kasar. Ya kuma ce majalisar za ta yi aiki wajen aiwatar da dokar masana’antun man fetur da gyara dokar zabe.

Mista Lawan ya ce majalisar attawa za ta yi hukunci kan inganta ma’aikatar wutar lantarki, cigaban ma’adinai da kuma habbaka fannin noma a fain kasar.

Hakan na zuwa ne a yayinda ya yi alkawarin cewa yan majalisar za su yi aiki tare da ma’aikatu, reshe da hukumomi domin tabbatar da aiwatar da cikakken kasafin kudin 2020.

Yayinda ya ke yiwa abokan aikinsa maraba da dawowa daga hutu, Mista Lawan ya bukace su da su kara kokari a wannan shekarar ta 2020.

An dage zaman bayan wani jawabi da Shugaban masu rinjaye a majalisa, Abdullahi Yahaya ya gabatar, inda ya roki abokan aikinsa da su dage zaman majalisar don karrama wani mamba na majalisar wakilai, Muhammadu Gawo, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Disamba.

Mista Gawo wanda ke wakiltan mazabar Garki/Babura da ke jihar Jigawa, ya rasu a kasar Dubai.

Marigayi dan majalisar ya kasance mamba na jam’iyyar All Progressives Congress kuma babban mamba a majalisar wakilan.

KU KARANTA KUMA: K’anin Sultan, Bala Abubakar, ya sha kashi a zaben da aka yi a Jihar Sokoto

Shugaban majalisar ya kuma roki abokan aikin nasa da su yi shiru na minti guda domin karrama marigayin.

Bayan nan sai aka dage zaman da misalign 12:00 na rana. Ana sanya ran za su dawo a gobe Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel