Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau

Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau

- Sanata Ibrahim Shekarau ya yi martani a kan rikicin da ke tsakanin masarautar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi 11 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje

- Shekarau ya ce suna iya bakin kokarinsu ta karkashin kasa domin ganin sun yi sulhu a kan lamarin wana ya ki ci ya ki cinyewa

- Ya ce a matsayinsa na dan majalisar masarautar jihar kuma jigo a gwamnatin bai kamata ya fito bainar jama'a ya yi tsokaci kan lamarin ba

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Ibrahim Shekarau ya yi martani a kan rikicin da ke tsakanin masarauta da gwamnatin jihar Kano. Ya ce yana iya bakin kokarinsa ta karkashin kasa don ganin an samu jituwa tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Muhammad Sanusi II.

A wata hira da ya yi da shafin BBC Hausa, Shekarau wanda ke wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, ya ce ba zai yiwu ya fito bainar jama’a da sunan yin tsokaci kan lamarin ba alhalin ya kasance an majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin jihar Kano.

Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau
Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau
Asali: Twitter

Shekarau ya jadadda cewa za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa don cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu.

Wannan shine karo na farko da sanatan ke magana tun bayan fara samun rashin jituwa a tsakanin shugabannin biyu yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.

Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau
Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau
Asali: Instagram

Ya ce: “Ita masalaha kamar ciwo ce, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba."

KU KARANTA KUMA: Motocin APC zan fara kamawa kan harajin hotunan jam’iyya – Shugaban Karota

Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta.

A baya mun ji cewa wata babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 27 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar da dattijan jihar Kano suka shigar ta neman a dakatar da sabuwar dokar kirkirar sabbin masarautu guda hudu a Kano.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa dattijan Kano su 19 a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Usman Tofa sun shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar sabuwar dokar da ta bawa gwamnatin Kano damar kirkirar sabbin masarautu.

Wadanda sunansu ya bayyana a karar da dattijan suka shigar sune kamar haka; shugaban majalisar dokokin jihar Kano, alkalin alkalai na jihar Kano, Tafida Abubakar Ila (sarkin Rano), Ibrahim Abdulkadir Gaya (sarkin Gaya), Dakta Ibrahim Abubakar II (sarkin Karaye), Aminu Ado Bayero (sarkin Bichi), fadar Kano da sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel