Katsina ta yi babban rashi da mutuwar Sarkin Yamma, Tukur Sa'idu – Inji Buhari

Katsina ta yi babban rashi da mutuwar Sarkin Yamma, Tukur Sa'idu – Inji Buhari

Mun samu labari cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jajantawa mutanen kasar Katsina a game da wani rashi da su ka yi a makon jiya.

Shugaban kasar ya aiko ta’aziyyarsa ta musamman ga gwamnatin jihar Katsina da Masarautar kasar da kuma al’umma da Iyalin Marigayi Sarkin Yamma.

Sarkin Yamman Katsina watau Hakimin Faskari ya rasu ne a Ranar Juma’ar da ya gabata kamar yadda mu ka samu labari daga bakin wasu ‘Yanuwansa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi a Ranar Litinin, 27 ga Watan Junairu, 2020, ya na mai cewa za a yi rashin wannan Dattijo da ya bar Duniya.

Shugaban kasar ya ce a lokacin rayuwarsa, Sarkin Yamma Mutum ne mai tsoron Allah da kuma kokarin kawo cigaba a Masarauta da jihar Katsina baki daya.

Buhari ya yi wannan jawabi ne ta bakin Malam Garba Shehu, wanda ke magana da yawunsa. Marigayin ya halarci jami'ar ABU Zariya tun a shekarar 1966.

KU KARANTA: 'Yan Arewa su na da ta cewa game da wanda zai zama Shugaban kasa

Katsina ta yi babban rashi da mutuwar Sarkin Yamma, Sa'idu – Inji Buhari
An ce Tukar Sa’idu ne Bakatsinen farko da ya fara karatu a King’s College
Asali: Facebook

Buhari ya ke cewa za a cigaba da tunawa da Marigayin saboda irin kokarin da ya yi wajen ganin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar Katsina.

Bayan haka Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya ce Sarkin Yamma ya kasance wani bango a wajen Sarkin Katsina, wanda zai yi rashin shawarwarinsa.

A karshen takaitaccen jawabin na sa, Buhari ya yi addu’a ga Sarkin Yamma tare da ba Iyalin Hakimin da sauran ‘Yanuwa da Abokan arziki jure wannan rashi.

Alhaji Muhammad Tukur Usman Sa’idu wanda ya mutu ya na da shekaru 76 a Duniya ya hau kan mulki ne tun cikin shekarar 1986, kenan ya shafe shekaru 34.

Marigayi Sarkin Yamman Katsina kuma Hakimin Faskari, Alhaji Tukur Usman Sa’idu mutum ne wanda ya dade ya na kira a hada-kan al’umma a jihar Katsina.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel