Sanata Ifeanyi Ubah ya na da takardar jarrabawa Inji NECO
Kwanaki goma bayan an tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga majalisar tarayya bisa zargin satifiket din bogi, hukumar NECO ta fito ta yi magana.
Hukumar jarrabawar kasa watau NECO, ta tabbatar da cewa Sanatan ya rubuta jarrabawar kammala sakandare, kuma ya lashe jarrabawar.
Mai girma Sanata Ifeanyi Ubah ne ya fitar da wannan labari a Ranar Litinin, 27 ga Watan Junairu, 2020 a shafinsa na sada zumunta na Facebook.
‘Dan majalisar da aka sallama ya ce hukumar NECO ta tabbatar da cewa takardun shaidar jarrabawarsa da ya gabatarwa INEC ba na jabu bane.
A cewarsa, a wata wasika da NECO ta aikawa kungiyar HURIWA ta Marubutan Najeriya, an tabbatar da sahihancin sakamakon jarrabawar sa.
Hukumar jarrabawa ta NECO ta fito da wannan wasika mai lamba ta NECO/R/LGS/20/003 a Ranar Alhamis da ta wuce, 23 ga Watan Junairun 2020.
Watakila wannan wasika ta taimaka wajen wanke ‘Dan majalisar mai wakiltar mutanen Yankin Kudancin jihar Anambra a jam’iyyar adawa ta YPP.
NECO ta tabbatar da cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya rubuta kwas takwas ne a jarrabawar da ya zana. Ga kuma sakamakon da ya samu a wancan lokaci:
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da Sanata Shehu Sani a gaban Alkali
1. Ingilishi C6
2. Lissafi C6
3. Ilmin halittu F9
4. Ilmin sha’anin gwamnati C6
5. Ilmin tattali C5
6. Adabin Turanci C5
7. Kasuwanci C5
8. Ilmin addinin Kirista C6
Jawabin hukumar ya ce: A kunshe da wannan sako akwai
1. Ainihin Satifiket din jarrabawa mai dauke da kwas bakwai da aka yi nasara, ba tare da kwas din da aka fadi ba.
2. Takardar sakamakon jarrabawa wanda za a iya tabbatarwa da katin NECO na N500. (Wanda zai zo da kwas din da aka fadi)
3. Wasikar neman samun takardar jarrabawa da satifiket.
4. Sakamakon jarrabawa mai dauke da kwas din da aka fadi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng