An rantsar da Gwamna Yahaya Bello a karo na biyu

An rantsar da Gwamna Yahaya Bello a karo na biyu

An rantsar da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu domin sake shugabancin jihar a karo na biyu a Lokoja, babbar birnin jihar.

Shugaban alkalan jihar ne ya rantsar da Bello tare da abokin takararsa a zaben watan Nuwamba, Edward Onoja, Channels TV ta ruwaito.

Taron ya samu halarta wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnati a sauran masu fada a ji.

Hukumar INEC ce ta kaddamar da Yahaya Bello dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashezaben gwamnan jihar Kogi.

Hukumar zaben ta bayyana cewa Bello na APC ya samu kuri’u mafi yawa a zaben wato guda 406,222 inda ya kayar da Musa Wada na PDP wanda ya samu kuri’u 189,704 a zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da belin Shehu Sani

A bangare guda, mun ji cewa Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP kamar yadda mu ke samun labari.

Wani daga cikin Masu ba gwamnan shawara, Mohammad Bello, shi ne ya sanar da Manema labarai wannan a wani jawabi da ya fitar ba da dadewa ba.

Malam Mohammed Bello ya tabbatar da zama gaskiyan rade-radin da aka dade ana yi cewa Aminu Waziri Tambuwal ne zai gaji kujerar Mista Seriake Dickson.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel