Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da belin Shehu Sani
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani.
Justis Inyang Ekwo ne ya bayar da belin Sanata Sani a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu a Abuja a lokacin gurfanar dashi kan tuhume-tuhume biyu na cin hanci da damfara.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta sanya tuhume-tuhumen a kansa.
Sai dai kuma Sanata Sani bai amsa tuhumar da ake masa ba yayinda lauyansa, A. Ibrahim ya nemi kotu ta bayar da belinsa.
Sai dai lauyan EFCC, Abbah Muhammed, ya ce ba a dade da bashi takardar sanar da belin ba.
KU KARANTA KUMA: Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)
Bayan sauraron jawaban lauyoyin biyu, Justis Ekwo ya dage sauraron zaman belin domin ba mai karar damar yin nazari a kai.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da tsohon dan majalisan dattawa da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a kotu.
An gurfanar da Shehu Sani ne da safiyar yau Litinin, 27 ga Junairu a babban kotun tarayya dake zaune a Abuja, birnin tarayya. Ana zargin shi da laifuka biyu: Karban cin hanci da damfara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng