Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)

Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)

Labarin wata mata yar asalin Najeriya na ganiyar yin tashe a shafukan sadarwa bayan hotunan auranta ya yi fice a shafin Facebook kasancewar ya samu masoyinta a karshe kuma sun yi aure tana da shekara 60 a duniya.

Duba ga labarin, za a iya cewa mutum baya taba rasa masoyinsa a cikin kowani yanayi.

Tana a tsakanin shekaru 60 kuma a jiya Lahadi ne ta yi auranta na farko.

Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)
Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta
Asali: Facebook

Wata mai amfani da shafin Facebook, Nneka ta wallafa hotunan tare da rubuta: "Kwarai Isaac da ni mun je kauye a jihar Anambra don shaida aure mafi kyau a wannan karnin. Goggo Nwatoka bata taba aure ba a rayuwarta. Ya kasance goggon Isaac daga bangaren mahaifinsa kuna daya daga cikin surukai mafi kyawu da mutum zai yi fatan samu. Ta kula da kakar mijina sosai har sai da ta mutu a ganiyar shekaru 90.

Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)
Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Harkar tsaro: Ya kamata a gayyato Shugaba Buhari zuwa Majalisa – Inji PDP

Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)
Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)
Asali: Facebook

"A koda yaushe ta kan kula da dukkanin ahlin idan muka je bikin Kirsimeti.... ko ni na cika da mamaki amma naji dadi a lokacin da kyakkyawan mutum kamar Mista Okeke ya zo neman auranta. Kuma a jiya suka yi aure a cocin St. Theresa Catholic Church a Enugukwu, jihar Anambra."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng