Jam’iyyar PDP ta sha kashi a zaben Majalisar da aka yi a Jihar Imo

Jam’iyyar PDP ta sha kashi a zaben Majalisar da aka yi a Jihar Imo

‘Yar jam’iyyar APC da ta shiga takaran zabe a Imo, Miriam Onuoha, ta samu nasarar tafiya majalisar wakilan tarayya domin ta wakilci Mazabarta.

Kamar yadda mu ka samu labari, Miriam Onuoha ta jam’iyyar APC ta doke babban abokin hamayyarta na jam’iyyar PDP, Hon. Obinna Onwubualiri.

Wannan nasara da APC ta samu a zaben Ranar Asabar, 25 ga Watan Junairun 2020, ya na nufin Misis Onuoha za ta canji Obinna Onwubualiri a Majalisa.

A sakamakon da hukumar zabe na kasa, INEC ta fitar, Onuoha ta samu kuri’u 23, 690 a zaben, yayin da Hon. Onwubualiri ya zo na biyu da kuri’a 10, 010.

‘Yar takarar ta jam’iyyar APC za ta wakilci mutanen Garin Okigwe da kewaye a majalisar wakilai kamar yadda jami’in hukumar INEC ya tabbatar jiya.

KU KARANTA: PDP ta tika Ministan Neja-Delta da kasa a mai-men zaben Akwa Ibom

Jam’iyyar PDP ta sha kashi a zaben Majalisar da aka yi a Jihar Imo
Obinna Onwubualiri ya rasa kujerarsa bayan kotu ta sa an sake zabe a Imo
Asali: Facebook

Frank Collins wanda ya sanar da sakamakon zaben a madadin hukumar INEC, ya bayyana cewa 19.06% na mutanen Mazabar ne kawai su ka fito zaben.

Mutane 200, 684 ne su ka yi rajista a Isiala Mbano/Onuimo/Okigwe, amma mutum 38, 244 ne kadai su ka fito domin kada kuri’arsu a wannan zabe.

Hukumar INEC ta bayyana cewa tazarar wanda ta yi nasara da wanda ya zo bayanta shi ne 13, 680. Jam’iyyu 28 su ka shiga wannan takara da aka yi.

An gudanar da zaben Yankin ne bayan kotun daukaka kara ta rusa zaben da aka yi a 2019. Jihar ta na cikin inda aka sake yin zabe a karshen makon nan.

Idan ba ku manta ba, a jiya mu ka samu labari cewa jam’iyyar APC mai mulki ta kuma lashe wata kujerar majalisar wakilan tarayya a jihar Kuros-Riba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel