Ni da Farfesa Osinbajo, abubuwa sumul su ke tafiya Inji Buhari
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana game da yadda alakarsa da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ta ke tafiya.
Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a wata Mujalla a jiya Lahadi watau Ranar 26 ga Watan Junairun 2020.
Buhari ya fadawa Mujallar ta The Interview cewa babu wani sabani da ake samu tsakaninsa da Mataimakin na sa, Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo.
An wallafa bayanin wannan hira ne a karshen makon da ya wuce, inda shugaban kasar ya tabo batutuwa da su ka shafi mulkinsa da kuma Najeriya.
A cikin hirar shugaban kasar da Mujallar The Interview, ya yi magana a kan zaben 2023 da kuma abubuwan da Janar TY Danjuma ya ke fada a kansa.
KU KARANTA: Buhari ya yi wa TY Danjuma raddi a kan sukar Gwamnatinsa

Asali: Facebook
Da aka tambayi shugaban kasar ya yi wa dangantakarsa da Mataimakinsa hisabi a mizani daga daya zuwa goma, sai ya ce alakar su kyakyyawa ce.
“Babu wata matsala, ko kuwa shi (Farfesa Yemi Osinbajo) ya kawo maku kuka ne? Shugaban na Najeriya ya ke tambayar ‘Yan jaridar a hirar ta su.
A game da harin 2023 da wasu ‘Yan siyasa su ke yi, Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu wannan kudiri, su maida hankali wajen cigaban kasa.
Bayan zabe, an yi ta rade-radin cewa an samu sabani tsakanin shugabannin har ta kai ana kokarin ragewa Yemi Osinbajo karfi a fadar shugaban kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng