Likitan jihar Jigawa ya kwaso zazzabin 'lassa' daga IDP a Maiduguri

Likitan jihar Jigawa ya kwaso zazzabin 'lassa' daga IDP a Maiduguri

Anthony Etim likita ne a jihar Jigawa da ke aiki da Doctors without Borders. An gano cewa ya harbu da cutar zazzabin Lassa bayan ziyarar da ya kai sansanin 'yan gudun hijira da ke Borno.

A yayin tabbatar da wannan cigaban ga jaridar Premium Times a ranar Lahadi, mukaddashin babban sakataren ma'aikatar lafiya ta jihar Jigawa, Salisu Mu'azu ya ce a halin yanzu an ware likitan a wani asibiti da ke karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.

Cibiyar kula da barkewar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an samu mace-macen mutane 29 da kuma wasu 195 da aka samu da cutar zazzabin Lassa a fadin jihohi 11 na kasar nan.

Daraktan cibiyar, Dr Chikwe Ihekweazu ya bayyana hakan ne a takardar da yasa hannu kuma ya fitar a ranar Asabar a garin Abuja.

Ya yi bayanin cewa wannan kiyasin na ranar Juma'a ne 24 ga watan Janairu. Ihekweazu ya ce an tabbatar da barkewar cutar kashi 89 cikin wadanda ake zargi a jihohin Ondo, Edo da Ebonyi. Shugaban ya ce a mayar da martanin cigaba da barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohin kasar nan, NCDC ta bude layin gaggawa a ranar Juma'a don daukar matakin gaggawa.

DUBA WANNAN: Annobar 'Lassa Fever': Mutane 29 sun mutu, 195 sun kamu a jihohi 11

Ihekweazu ya ce layikan gaggawan sun hada da na NEMA, ma'aikatar noma da raya karkara, WHO, UNICEF da wasu cibiyoyin lafiya na Amurka. Ya ce NCDC din za ta cigaba da tallafawa jihohin da wannan cutar ta fada.

Ya ce hukumar ta tura rundunar taimakon gaggawarta zuwa jihohi biyar da aka fara samun barkewar cutar. Kamar yadda daraktan ya sanar, ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire ya jagoranci wasu wakilai zuwa jihar Kano a ranar Asabar bayan mutuwar wasu ma'aikatan lafiya biyu sakamakon cutar.

Hukumar ta kara inganta sadarwa tsakaninta da yankunan da cutar ta fara bullawa tare da tabbatar da wayar da kai ga jama'a a kan hanyoyin gujewa cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng