Sanata Ekpenyong ya doke Akpabio a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom

Sanata Ekpenyong ya doke Akpabio a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom

Jam’iyyar PDP ta yi nasara a zaben Majalisar Tarayya da hukumar zabe na kasa watau INEC ta gudanar a jihar Akwa Ibom a karshen makon nan.

Rahotanni sun ce PDP ce ta lashe kujerun majalisar dattawa da ta majalisar wakilai da kuma ta majalisar dokoki a jihar Kudu maso Kudancin kasar.

An gudanar da zaben ne a cikin karamar hukumar Essien Udim kacal. Amma duk da haka, an yi ta fama da rikici da hatsaniyar ‘Yan bangar siyasa.

Tashin hankalin da aka gamu da shi ya kai har an sace wani Malamin zabe a Mazabar da Godswill Akpabio na APC ya fito, wanda a karshe aka sake shi.

A zaben Sanatan Akwa Ibom na Arewa maso Yamma, Chris Ekpenyong na jam’iyyar PDP mai rike da mulkin jihar, shi ne ya kara samun nasara a jiya.

Sanatan mai-ci ya doke tsohon gwamna Godswill Akpabio wanda ya rasa wannan kujera a zaben 2019 bayan ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

Sanata Chris Ekpenyong ya samu kuri’u 134,717, yayin da Godswill Akpabio wanda tuni ya zama Ministan Neja-Delta ya tashi da kuri’u 83,820.

KU KARANTA: PDP ta tashi da kujerun Majalisa a Jihohin Kaduna da Bauchi

Sanata Ekpenyong ya doke Akpabio a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom
Ta tabbata Sanata Akpabio ba zai koma Majalisar Dattawa ba
Asali: Facebook

Hukumar INEC mai gudanar da zabe na kasa ta fitar da wannan sakamako a safiyar Ranar Lahadi, 26 ga Watan Junairun 2020 kamar yadda mu ka ji.

A zaben kujerar Yankin Ikot Ekpene/Essien Udim/Obot Akara a Majalisar wakilai, jam’iyyar PDP ce ta yi nasara da ratar kuri’u kusan 23, 000.

Nsikak Ekong shi ne ya zo na farko da kuri’a 45,366 a PDP. Jam’iyyar APC wanda ta ke biye ta samu kuri’u 22, 757 ne ta hannun Emmanuel Akpan.

A Mazabar Essien Udim, PDP ta samu kuri’a 18,999, APC kuwa ta samu 7,108. Hakan na nufin Esse Umoh ya doke Nse Ntuen a kujerar majalisar dokoki.

Yunkurin Sanata Akpabio na komawa Majalisa bai yiwu ba a sakamakon nasarar Ekpenyong. Dama can Ministan ya nuna rashin sha’awar sake takara.

Emmanuel Akpan ya nuna cewa bai yarda da aikin Kwamishinan zaben Yankin ba watau Mike Igini. Wannan ya sa ya fita daga takarar ana daf da zaben.

Shi ma Nse Ntuen na APC ya janye kansa daga takarar ya na mai ikirarin cewa kotu ba ta bada umarni a sake gudanar da zaben da ya riga ya yi nasara ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng