Salihu, Ojezua sun gaza tsige Shugaban jam’iyyar APC daga kujerarsa a kotu

Salihu, Ojezua sun gaza tsige Shugaban jam’iyyar APC daga kujerarsa a kotu

Babban kotun tarayya da ke Garin Abuja, ya ki bada dama kamar yadda wani shugaban jam’iyya ya bukata na sauke Adams Oshiomhole.

Mustapha Salihu shugaban APC na Arewa maso Gabas da tsohon shugaban APC na Edo, Anselm Ojezua, ba su yi nasarar sauke shugaban ba.

Salihu, Ojezua da wasu Jiga-jigan jam’iyyar APC ne su ke kokarin ganin kotu ta sallami Oshiomhole daga ofis bayan dakatar da shi.

Oluwole Afolabi, Mustapha Salihu, da Ojezua sun fadawa kotu cewa a hana Oshiomhole tsaida kansa a matsayin shugaban jam’iyya na kasa.

Bugu da kari, masu karar sun nemi Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya da shugaban DSS na kasa da su hana Adams Oshiomhole shiga ofishinsa.

KU KARANTA: Buhari bai yi wa Tinubu alkawarin mika masa mulki ba - Moghalu

Da aka fara shari’ar a kotu, babban Lauyan shugaban APC da jam’iyya, D. D. Dodo (SAN), ya fadawa kotu cewa ba su san inda a kwana ba.

Alkali mai shari’a Danlami Zama Senchi ya bayyana cewa zai saurari korafin kowane bangare kafin ya bada umarnin yin abin da ake bukata.

Kotu ta bukaci wadanda su ka shigar da karar su dakata kafin a fara sauraron korafinsu. An dage shari’ar zuwa Ranar 18 ga Fabrairun 2020.

Idan ba ku manta ba, Mustafa Salihu ya zargi shugaban jam'iyyar na kasa da karfa-karfa wajen nada sabon Sakataren jam'iyya Waziri Bulama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel