Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, inda APC ta yi nasara a Cross River

Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, inda APC ta yi nasara a Cross River

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da nasarar Comfort Amwe ta jam'iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben maye gurbi na mazabar Sanga a majalisar jihar Kaduna.

Baturen zabe, Salihu Kargi na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya sanar da sakamakon a Gwantu a ranar Lahadi. Ya ce Amwe ta samu kuri'u 19,815 inda tayi nasarar lallasa Haliru Gambo-Dangan na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 19,688.

Anyi zaben maye gurbin ne a rumfunan zabe 14 na karamar hukumar Sanga.

A karamar hukumar Kagarko kuwa, tsohon kakakin majalisar jihar Kaduna, Nuhu Goro Shadalafiya ne ya lashe zaben kujerar mazabar a majalisar jihar. Shadalafiya na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 24,658 inda Tanko na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 20,206.

Hakazalika dan takarar jam'iyyar PDP, Alhaji Madaki Gololo ne ya lashe zaben maye gurbin mazabar tarayya ta Gamawa da ke jihar Bauchi wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

A yayin sanar da sakamakon zaben a garin Gamawa a ranar Lahadi, baturen zabe, Dr Abubakar Mayin na jami'ar tarayya da ke Dutse, ya ce Gololo ya samu kuri'u 21,223 inda ya kayar da abokin adawarsa Isa Wabu na jam'iyyar NNPP da ya samu kuri'u 15,004.

Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, inda APC ta yi nasara a Cross River
Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, inda APC ta yi nasara a Cross River
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi: Dattijan APC a Kano sun juya wa Kofa baya, dan takarar PDP na kan hanyar lashe zabe

Sauran 'yan takarar da suka nemi kujerar amma suka sha mugun kaye sun hada da Dahiru Alhaji na jam'iyyar ACP, Mustapha Ahmed na jam'iyyar GPN, Ibrahim Aliyu na jam'iyyar MP da kuma Bashir Dogowa na jam'iyyar ADC.

A jihar Cross River, INEC ta bayyana Alex Egbonna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar tarayya ta Yakurr/Abi da ke jihar.

Kwamishinan zabe na jihar, Dr Alalibo Johnson ya sanar da sakamakon a ranar Lahadi a Ugep da ke karamar hukumar Yakurr ta jihar.

Alalibo ya ce dan takarar jam'iyyar APC ya samu kuri'u 29,716 inda ya doke abokin hamayyar shi na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 26,039.

Kwamishinan ya bayyana Davies Etta na jam'iyyar PDP a matsayin wanda yayi nasara a mazabar Abi ta majalisar jihar.

Dan takarar PDP din ya samu kuri'u 13,349 inda ya doke abokin adawarsa na jam'iyyar APC mai kuri'u 8,792.

Kwamishinan zaben ya ce sakamakon tashin hankula da aka samu a gundumar Afafanyi/Igonigoni mai rumfunan zabe 8, an soke zaben gundumar gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel