Valencia ta ragargaji Barcelona 2-0 a filinta a wasan farko a La-liga tun 2007

Valencia ta ragargaji Barcelona 2-0 a filinta a wasan farko a La-liga tun 2007

A Ranar Asabar ne sabon Mai horaswa Quique Setien ya gamu da rashin nasararsa ta farko a kungiyar Barcelona tun da aka dauke sa haya.

A wasannin farko, Koci Quique Setien ya doke Granada da Ibiza a gasar La-liga da Copa del Rey. Sai dai abubuwa sun jagwalgwale a makon nan.

Barcelona ta dauki kashinta a hannu ne a wasan da ta buga da Valencia jiya. An doke Zakarun ne da ci biyu da nema ta hannun Maximillano Gomez.

Duk da haka, Ter Stegen ya tare bugun finariti daga kafar Gomez kafin a tafi hutun rabin lokaci. Da alamun ba don haka ba da abin ya zarce haka.

Rahotanni sun ce Barcelona ta dawo hutun rabin lokaci kamar da gaske bayan Messi ya dawo da karfinsa, daga baya kuma aka koma gidan jiya.

KU KARANTA: Ba zan kashe kai na a kan Kungiyar Arsenal ba - Atiku Abubakar

Valencia ta ragargaji Barcelona 2-0 a filinta a wasan farko a La-liga tun 2007
'Yan wasan Valencia sun yi wa Barcelona tauri a gida
Asali: Getty Images

‘Dan wasan Barcelona, Ansu Fati ya zo kiris da zura kwallo a raga amma ya jefawa Jaume Domenech da ke cikin ragar Valencia a hannusa.

Lionel Messi ya buga wasan, amma rashin Luis Suarez wanda zai dauki lokaci ya na jinya, ya na cigaba da kawowa kungiyar cikas a wasanninta.

Tsohon ‘dan wasan Arsenal, Gabriel Paulista, ya yi tunanin ya zurawa Barcelona ta uku, kafin ya fahimci cewa Alkalan wasa sun kashe wannan ci.

Wannan ne wasan farko da Valencia ta doke Barcelona a filin Mestalla tun shekarar 2007. Idan Real Madrid ta ci wasan yau, za ta ba da ratar maki uku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel