Tsarin mulki, harkar zabe, LGAs, binciken MDAs, da sauran aikin da ke kan Majalisa

Tsarin mulki, harkar zabe, LGAs, binciken MDAs, da sauran aikin da ke kan Majalisa

Jaridar nan ta Daily Trust ce ta fara jero wasu manyan ayyuka da majalisar wakilan tarayya da dattawan kasar nan za su fuskanta a wannan shekara ta 2020.

Ga wasu daga cikinsu:

1. Garambawul a tsarin mulki

Ana sa ran cewa kwanan nan ‘Yan Majalisar Najeriya za su fara shirin yi wa kundin tsarin mulki garambawul. A cikin wannan Watan za a soma wannan aiki da zarar an kafa kwamitin.

2. Harkar zabe

Wani bangare da za a taba shi ne sha’anin zabe a Najeriya. ‘Yan Majalisa sun yi yunkurin sake tsarin zaben kasar a lokacin Bukola Saraki amma ba su yi nasara ba daga wajen shugaban kasa.

3. Aron kudi

Wani babban abu da ke teburin ‘Yan majalisar shi ne kokon barar shugaban kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin Dala 29.96. A majalisar baya Sanatoci sun yi fatali da wannan roko.

4. Sababbin kudirori

Daga cikin kudirorin da ake neman jin yadda za a kare da su a majalisa akwai wanda zai taka masu yada kalaman kiyayya da wanda ke neman sa takunkumi a kafafen sadarwan zamani.

KU KARANTA: APC ta sha kashi a hannun PDP a zaben Majalisa a Jihar Bauchi

Tsarin mulki, zabe, binciken MDAs, da sauran aikin da ke kan Majalisa
Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Lawan a bakin aiki
Asali: Twitter

5. Binciken MDAs

Bincike kan yadda hukumomi da ma’aikatun gwamnati su ke tafka barna ya na cikin aikin da ke gaban majalisa a 2020. Wannan duk ya na cikin hurumin da doka ta tsagawa 'Yan Majalisa.

6. Kananan hukumomi

A 2020 ake tunanin za a karkare ba kananan hukumomi cikakken ‘yanci daga hannun jihohi. Idan aka yi haka za su samu damar zaben shugabanninsu, daukar ma’aikata da iko da kudi.

7. Gyaran N37b

Mutane da-dama sun zura idanu su ga yadda Majalisar Najeriya za ta batar da kudi har Naira biliyan 37 domin yi wa haraba da cikin zauren majalisar wasu kwaskwarima da gyare-gyare.

8. Zaftare yawan MDAs

Akwai kuma yiwuwar ragewa ma’aikatun kasar sama da 600 yawa wanda ake ganin cewa su na ci wa gwamnati kudi sosai. Akwai kuma batun wasu hukumomin yanki da ake faman kafawa.

9. Nadin mukamai

Sanatoci da sauran ‘Yan majalisa sun zura idanu domin ganin yadda shugabanninsu za su kasa wasu kujeru da yanzu babu wadanda ke kai a sakamakon korar wasu ‘Yan majalisar da kotu ta yi.

10. PIB

Kudirin PIB wanda ya shafe shekara da shekaru ya na yawo a majalisa ya na cikin abubuwan da Majalisa za ta taba a bana. Idan wannan kudiri ya fara aiki, zai gyara harkar mai a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng