Duk da banbancin jam’iyya, Gwamna Umahi ya ce babu wanda ya isa ya tsige Obaseki

Duk da banbancin jam’iyya, Gwamna Umahi ya ce babu wanda ya isa ya tsige Obaseki

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ba da tabbacin cewa za a sake zabar Godwin Obaseki a matsayin gwamnan jihar Edo

- Umahi ya ce babu abun da zai hana gwamnan zarcewa saboda ya yi kokari sosai kuma ya cancanci cigaba da shugabanci

- Obaseki ya kasance dan jam’iyyar All Progressive Congress(APC) yayinda Umahi ya kasance dan jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP)

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu ya ba da tabbacin cewa za a sake zabar Godwin Obaseki a matsayin gwamnan jihar Edo.

Ya ce babu abun da zai hana gwamnan zarcewa saboda ya yi kokari sosai kuma ya cancanci cigaba da shugabanci.

Obaseki ya kasance dan jam’iyyar All Progressive Congress(APC) yayinda Umahi ya kasance dan jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP).

Umahi ya fadi hakan ne da yake jawabi ga matar Obaseki, Besty da sauran matan gwamnonin kudu wadanda suka kai masa ziyarar bangirma a Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi.

Matan gwamnonin sun je jihar ne domin taron kungiyar matan gwamnonin kudancin Najeriya da ake yi.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 5 da Kwankwaso ya fada a martaninsa ga Kotun Koli

Gwamnan na Ebonyi ya ayyana cewa Allah ne ke bayar da mulki ba mutum ba, don haka ko yaya aka yi kokarin hana Obaseki ba zai cimma nasara ba sai abun da Allah ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng