Muhimman abubuwa 5 da Kwankwaso ya fada a martaninsa ga Kotun Koli

Muhimman abubuwa 5 da Kwankwaso ya fada a martaninsa ga Kotun Koli

Kamar yadda kuka sani kotun koli dai ta yanke hukunci a kan zaben gwamnan Kano, inda ta jadadda wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kujerarsa. Bayan haka PDP ta ce ta amince da hukuncin da zuciya daya.

Haka ma Kwankwason ya yi martani game da wasu batutuwa da suka shafi hukuncin Kotun Kolin da kuma dangantakarsa da 'yan jam'iyya mai mulki a jihar.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya bayyana:

1. An yi wa Abba 'fashi da makami'

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa sun tsayar da Abba zabe kuma ya ci zabe amma an yi musu fashi da makami.

Ya bayyana cewa shi a matsayinsa na dan siyasa, kwana yake yana godiyar Allah domin duk wata hujja ya bayar, amma abin da alkalai da INEC suka fada, shi ne ''zubar da girma'', inda ya kara da bayyana cewa kowa ya san gaskiya.

A yayin hirar a ka yi dashi, Kwankwaso ya bayyana cewa duk mutumin da yake jihar Kano ya san an zalunce su kan harkar zabe.

2. Kan dalilin da ya sa makusantansa ke barinsa

A kan haka, Kwankwaso ya bayyana cewa bai cika son yi magana dangane da yaransa na siyasa ba domin duk wanda ya yi gaba to ya yi gaba amma duk da haka ya bayyana cewa dukkan masu barin jami'iyyar 'so suke yi su zama kamar Rabiu Kwankwaso''.

Ya bayyana cewa saboda soyyayar da ake yi masa ko kasuwa ya shiga mai tumatir ko kayan miya zai iya miko masa domin ya je gida ya yi miya saboda soyayya ko da ba shi da ko sisi.

Ya bayyana cewa duk wadanda suka fita daga cikin Kwankwasiyya, babu wani laifi da ya yi musu, kuma har yanzu yana son su duk da sun fita.

3. Hakuri a siyasa

A cikin bayanin nasa, ya bayyana cewa hakuri na da muhimmanci a siyasa. Ya ce hakuri da rage hassada na da matukar muhimmanci, inda ya bayar da misali da cewa idan Allah ya ba mutum abu zai yi murna, shi ma Allah zai ba shi wata rana.

Ya bayyana cewa duk wadannan rigingimu da suka taso a halin yanzu, a wurinsa ba su da amfani ko kadan.

Kwankwaso ya bayyana cewa ba shi ya shirya wadannan rigingimun ba, amma a cewarsa, 'shi shugaba na cike da shiga hatsari na abin da ba ka ce ba a ce ka ce".

4. Zargin da ake yi masa na 'son kai'

A tambayar da aka yi masa kan cewa 'yan bangaren adawa na zargin sa da yawan 'son kai' kuma abin da Kwankwaso ya 'shuka ne yake girba', Kwankwason ya mayar da martani kuma ya shaida cewa idan batun shuka ne ai shi ya shuka masu fadin wannan maganar kuma ga shi nan suna ta yaduwa da kasaita.

Ya bayyana cewa ''idan mafadin magana wawa ne majiyinta ba wawa bane.''

Ya bayyan cewa duk masu fadin irin wannan maganar ya yi musu komai a duniya, watakila ma a cewarsa wurin kyautatawa irin ta duniya daga 'mahaifinsu sai shi'.

KU KARANTA KUMA: Sauya-sheka: Ficewarsu Bichi ba ta yi mana dadi ba – Inji Rabiu Kwankwaso

5. Babban burinna a rayuwa

A cikin hirar, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa babban burinsa a rayuwa shi ne duk wanda yake tare da shi tun daga kan dan aike ya daga shi ya zama babba, kuma babba kololuwa, kamar yadda ya bayyana a turance ya ce ''Chief Exectuive Officer''.

Ya ce a rayuwarsa yana so ya ga mutumin da yake tare da shi ya wadata, kuma har ya wuce shi a wajen wadata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel