Sauya-sheka: Ficewarsu Bichi ba ta yi mana dadi ba – Inji Rabiu Kwankwaso

Sauya-sheka: Ficewarsu Bichi ba ta yi mana dadi ba – Inji Rabiu Kwankwaso

Fitaccen tsohon gwamnan Kano watau Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana game da juyin da aka samu a cikin tafiyar jam’iyyar PDP a jihar.

A Ranar Alhamis, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jawabi game da ficewar wasu Dakarun Kwankwasiyya da ake ji da su a jam’iyyar hamayya.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna cewa bai ji dadin barin shugaban PDP ,Rabiu Sulaiman Bichi da wasu daga tafiyar su ta Kwankwasiyya ba.

Tsohon gwamnan yake cewa ko da jariri ne ya fice daga jirginsu, ya na takaici saboda ganin al’umma su ne jarinsa a harkarsa ta siyasa.

Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya hira da ‘Yan gidan rediyo a cikin daren Alhamis, 23 ga Watan Junairun 2020 a gidansa.

Fitaccen ‘Dan siyasar ya bayyana cewa wadanda su ka hada-kai da Abdullahi Ganduje, su ka koma jam’iyyar APC ba za su samu komai ba.

KU KARANTA: Abba Gida-Gida ya yi magana bayan barin wasu kusoshin Kwankwasiyya

A game da zargin da ake yi masa na son kai da cewa ya shuka irin abin da ya faru, sai ya ce ‘Ya ‘yan APC ya shuka wanda yanzu sun tofo.

Injiniya Kwankwaso ya ke cewa duk masu cewa bai yi masu komai ba, kila duk Duniya bayan Mahaifansu, ya fi kowa tasiri a rayuwarsu.

A hirar, an tabbatar da cewa wata daga cikin ‘Yan Kwankwasiyyar da ta yi mubaya’a, Aisha Kaita, ta dawo daga rakiyar kwana guda da ta yi.

A game da Mai magana da yawunsa, Binta Sipikin, Kwankwaso ya ce za a iya mata uzurin sauya-sheka, saboda ma’aikaciyar gwamnati ce.

Tsohon Sanatan ya koka da abubuwan da ke faruwa a kasar tare da kira ga Masoyan PDP su tashi tsaye a zaben kujerun majalisun da za ayi.

Duk da wannan rashin da PDP ta yi daf da zabukan da za a sake yi a jihar, Rabiu Kwankwaso ya na ganin cewa PDP ce za ta yi nasara a gobe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel