Harkar tsaro: Ba mu yi kokari ba a matsayinmu na shugabanni – Ortom

Harkar tsaro: Ba mu yi kokari ba a matsayinmu na shugabanni – Ortom

Gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom ya amince cewa shugabannin Najeriya sun gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kasar nan.

Gwamna Samuel Ortom ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci wani taro da kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya a cikin makon nan.

Daily Trust ta rahoto cewa Kungiyar ta kai masa ziyara ne domin taya sa murnar nasarar da ya samu a game da shari’ar zaben 2019 a kotun koli.

Mista Ortom ya koka kan yadda ‘Yan ta’adda su ka hallaka shugaban kungiyar CAN na reshen jihar Adamawa a Ranar Litinin, Lawan Andimi.

“Bari in yi wa Kiristocin Najeriya jaje, musamman mutanen karamar hukumar Michika a jihar Adamawa, game da kisan shugaban CAN.”

KU KARANTA: An yi fashi a kamfanin MTN, an yi awon gaba da kudi

"Wannan babban rashi ne." A cewarsa, wannan kisan gilla ya nuna cewa babu wanda ya ke cikin kwanciyar hankali a fadin kasar nan.

“Bari in roki Kiristocin kasar nan da su dage da yi wa Najeriya addu’o’i saboda halin rashin tsaron da ake ciki a kasar ya na bukatar addu’a.”

“Ana fama da kashe-kashe a kowane bangare na kasar nan. Daga Legas zuwa Borno, a Enugu ko Abuja, har Katsina (jihar Buhari ba a kyale ba)"

“’Yan Najeriya ba su jin dadin kashe-kashen da ake yi, babu wanda zai iya barci da minshari. Duk shugabanninmu har da ni sun gaza kare jama’a.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel