Jihohin Arewa na tsakiya su na tunanin kirkiro Jami’an tsaro a Yankinsu

Jihohin Arewa na tsakiya su na tunanin kirkiro Jami’an tsaro a Yankinsu

Yayin da Najeriya ke cigaba da fama da matsalar rashin tsaro, gwamnonin yankin Arewa ta tsakiya sun fara wani sabon yunkuri a kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari a Yau Alhamis, gwamnonin tsakiyar Najeriyar sun zauna domin ganin yadda za su kawo zaman lafiya.

Kowane daga cikin Gwamnonin yankin ya samu halartar zaman musamman da aka yi a game da sha’anin tsaron da ya ke damun jihohin.

Masu ruwa da tsaki wajen kawo zaman lafiya sun halarci zaman. An yi wannan taro ne a Garin Lafia da ke jihar Nasarawa a makon nan.

A jawabin da gwamnonin su ka fitar bayan zaman, sun yarda cewa za su taimakawa ‘Yan Sanda da jami’an da su rika sintiri a Yankun na su.

KU KARANTA: Wani Sanatan Arewa ya koka da yadda ake kashe mutanensa

Bayan nan kuma an ci ma matsaya cewa gwamnonin na Nasarawa da kewaye za su rika zama sau uku a shekara domin duba lamarin tsaro.

Bugu da kari, gwamnatocin jihohin yankin za su kara himma wajen kawo shirye-shirye da za su taimaka wajen inganta rayuwar marasa galihu.

Daga cikin matakan da gwamnonin su ka dauka shi ne za su yi kokari wajen ganin duk wadanda ke sansanin gudun hijira sun koma gidajensu.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin za su kafa wasu Dakaru na PMD da CTU da za su yi maganin ta’addanci da ta’adin da ake fuskanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel