Ya yanke jiki ya sume saboda bai samu ganin Adam Zango ba bayan ya yi tattaki daga Sokoto zuwa Kauna (hotuna)

Ya yanke jiki ya sume saboda bai samu ganin Adam Zango ba bayan ya yi tattaki daga Sokoto zuwa Kauna (hotuna)

Masu iya magana sun ce soyayyar gamuwar jini ce, hakan ce ta kasance da wani bawan Allah mai suna Saifullahi Sayyinna wanda ya kasance masoyi ga shahararren tsohon dan wasan nan na Kannywood kuma mawakin zamani Adam A. Zango.

Saifullahi dai ya yi tattaki ne tun daga jihar Sokoto zuwa Kaduna domin kawai yaga masoyin nasa Adam Zango.

Sai dai kuma matashin ya je har kofar gidan jarumin amma bai sami ganinsa, ana haka kawai sai ya yanke jiki fadi sumamme.

Hakan ya sa daga bisani ya samu ganin jarumin nasa harma ya nemi su yi hoto domin nunawa mutanen garinsu cewa burinsa na ganin Adamu ya cika.

KU KARANTA KUMA: Abdulmumin Jibrin ya saduda, yana neman sulhu da shugabannin APC gabannin zaben da za a sake (bidiyo)

Adam zango ne ya wallafa labarin tare dda hotunan da suka dauka da mutumin a shafinsa na Instagram inda ya ke cewa: “Lallai so ba karya bane__ALLAH ke daura bawansa soyayya ko yana so ko baya so!!

“Wannan bawan ALLAN daga sokoto sayyinna yake, ya shigo garin kaduna domin kawai yaga Adam Zango. ALLAH da ikonsa yazo kofar gidana bai sami ganina ba sai ya yanke jiki fadi ya suma. Daga karshe dai ya sami ganina kuma har mun dauki hoto domin ya nunawa yan garinsu cewar ya ga masoyin shi ido da ido...SAIFULLAHI SAYYINNA kenan ALLAH ya bar soyayya!!”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng