An yi mace-mace bayan 'Yan Boko Haram da ISWAP sun juya juna baya

An yi mace-mace bayan 'Yan Boko Haram da ISWAP sun juya juna baya

Arangama tsakanin kungiyoyin yan ta’adda biyu a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanaiyar mutuwar mayaka da ama, wasu majiyoyi biyu suka bayyana hakan ga kafar labarai ta AFP hakan a ranar Litinin.

Mayaka a manyan motoci daga bangaren Boko Haram masu biyayya ga Abubakar Shekau sun far ma wani sansani mallakar abokan adawarsu ta ISWAP, wanda ya yi sanadiyar musayar wuta day a haddasa mutuwar wasu da dama, inji majiyar.

Mayakan na Boko Haram sun kai hari sansanin da ke kauyen Sunnawa a yankin Abadam da ke kusa da iyakar Nijar don kwato matansu da mayakan ISWAP suka kwace a harin da suka fara kaiwa sansaninsu da ke iyakar Nijar.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa rikicin wanda ya afku na kan bayyana a hankali-a hankali saboda karancin sabis din waya a yankin karkaran.

Da farko dai mayakan ISWAP sun kai hari wani sansanin Boko Haram a yankin Diffa da ke makwabtaka na Nijar inda suka yi garkuwa da mata 13.

KU KARANTA KUMA: Sanata Nazif ya ce babu makawa sai PDP ta kwato kujarar Shugaban kasa a 2023

Sai Boko Haram suka bibiyi matan zuwa Sunnawa a yankin tafkin Chadi wanda ke a karkashin ikon ISWAP sannan suka yanke shawarar kwato su, inji majayar. “Hakansu bata cimma ruwa ba domin har yanzu matar na a hannun wadanda suka yi garkuwa da su,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel