Sabon salo: 'Yammata da zawarawan arewa sun nemi a fara yi wa maza gwajin hankali kafin aure

Sabon salo: 'Yammata da zawarawan arewa sun nemi a fara yi wa maza gwajin hankali kafin aure

Yan mata da matan aure sun bukaci a fara yi wa maza gwajin hauka kafin aure saboda yawan dukan mata da maza keyi.

A cigaba da shirin Daga shafukan Instagram na gidan rediyon Dabo FM wannan ta ke lekawa shafin nan da mata da mazan Arewa ke tattaunawa a kan matsalolinsu na samar da 'yammata ko kuma ma'aurata, ta gano cewa matan sun bayyana bukatarsu ta a fara yi wa maza gwajin hauka kafin aure.

'Yammatan sun bayyana cewa su fa gaskiya an fara kai su makura ta yadda maza a zamanin nan ke jibgar matansu kamar kayan wanki.

DUBA WANNAN: Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja

A cewar wata "masu matsalar kwakwalwa yanzu sun dena bin bola, babbar riga suke sakawa kuma su yi hidindimu irin na mutane masu hankali. Kamata yayi a dinga dubawa, shin zai iya rike auren?"

'Yammatan sun koka a kan yadda 'yan uwansu da kawayensu ke basu labarai kan matsalolin da suke fuskanta a gidajen aurensu ko kuma a zamantakewarsu ta aure.

"Idan ba a duba kwakwalwarsu ba ta yaya za a gane mugunta ake yi mana ko kuma rashin hankali ne ke damun kwakwalwarsu?" cewar wata matar aure.

Wasu daga cikin matan sun bukaci har da mazan auren ba samari ba kadai, a dinga mika su lokaci zuwa lokaci don a duba kwakwalwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel