Tubabbun 'yan bindigan Zamfara sun nemi afuwa

Tubabbun 'yan bindigan Zamfara sun nemi afuwa

- Shugabanin 'yan bindigan Zamfara da suka tuba suka ajiye makamansu sun nemi mutanen Zamfara su yafe musu

- Shugabanin tubabbun 'yan bindigan sun yi wannan jawabin ne yayin wani taron sulhu da aka yi karkashin kwamishinan 'yan sanda Usman Nagogo

- Shugabanin sun bukaci mutanen masarautar Dansadau da suka tsere daga gidajensu su dawo kana manoma su koma gonakinsu su cigaba da ayyukansu

Manyan shugabannin tubabbun 'yan bindiga a Bindin-Dansadau na karamar hukumar Maru a jihar Zamfara sun nemi afuwa daga mutanen garurruwan da manoma da suka dade suna kaiwa hari na tsawon shekaru.

Shugabanin 'yan bindigan da suka hada da Damina da Wadalle da suka yi jawabi wurin taron sulhu da aka yi a karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sanda, Mr Usman Nagogo kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Kano: Dattijan APC sun bayyana matsayarsu a kan zaben maimaici na Kiru/Bebeji

Damina ya ce: "Muna neman afuwan dukkan wadanda suka fuskanci wahalhalu sakamakon hare-haren mu. Dukkan wadanda suka tsere daga gidajensu su dawo. Manoma su koma gonakin su su fara aiki, kada su ji tsoron komai."

Tubabbun 'yan bindigan kuma sunyi jawabi mai tsawo inda suka tabbatarwa kwamitin sulhun cewa sun amince da yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da zaman lafiya.

Sunyi kira da mutanen masarautar Dansadau da suka tsere daga gidajensu su dawo kana manoma da suka kauracewa gonakinsu su koma su cigaba da ayyukansu kamar yadda suka saba a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel