Yansanda sun halaka masu garkuwa da mutane 2, sun ceto mutum 20 a Kaduna

Yansanda sun halaka masu garkuwa da mutane 2, sun ceto mutum 20 a Kaduna

Akalla mutane 8 da wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba dasu a kan titin Kaduna zuwa Zaria a ranar Laraba sun kubuta sakamakon samame da jami’an rundunar Yansandan Najeriya suka kaddamar a kan miyagun.

Haka zalika Yansandan sun ceto wasu mutane uku dake aiki da kamfanin sadarwa na Airtel da aka sace su a ranar Talata, da kuma wasu mutane 9 da aka sace su tun a ranar 14 ga watan Janairu yayin da yan bindiga suka kai ma ayarin motocin Sarkin Potiskum hari.

KU KARANTA: Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, Yakubu Sabo ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda yace Yansanda sun kashe yan bindiga 2 a yayin samamen.

Sabo yace mutane 8 da aka sace a kan titin Kaduna zuwa Zaria suna kan hanyarsu ta zuwa babban birnin tarayya Abuja ne a cikin motarsu kirar Sharon a lokacin da yan bindigan suka tare motarsu. “Samun rahoton lamarin keda wuya sai muka tura jami’anmu dauke da makamai domin su bi sawun yan bindigan.

“A haka suka yi gaba da gaba da yan bindigan, inda aka yi musayar wuta, wanda ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga guda 2, sa’annan muka ceto mutane duka su 8 ba tare da wata matsala ba, yayin da sauran yan bindigan suka tsere da rauni daban daban a jikkunansu.” Inji shi.

Mutanen da Yansanda suka ceto sun hada da: Aisha Umar, Samira Ibrahim Dakata, Safiya Idris, Hauwa Aliyu, Aisha Yakubu, Ma’aru Adam, Safiya Audu, da Yahaya Bello, dukkaninsu daga jahar Kano suka fito.

Daga karshe Sabo yace Yansanda suna cigaba da bin sawun yan bindigan da nufin tabbatar da sun kamasu tare da gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci fushin hukuma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel