Sokoto: Hon. Bature Lili ya koma Jam’iyyar PDP mai mulki a Binji

Sokoto: Hon. Bature Lili ya koma Jam’iyyar PDP mai mulki a Binji

Mun samu labari cewa ‘Dan takarar jam’iyyar APC a zaben kujerar majalisar dokoki da za a karasa a jihar Sokoto, Alhaji Bature Lili, ya sauya-sheka zuwa PDP.

Bature Lili da dinbiyan Magoya bayansa sun tattara ina su-ina su, sun bar jam’iyyar APC mai adawa inda su ka koma cikin tafiyar PDP da ke mulki a jihar.

Honarabul Bature Lili wanda ya ke neman sake karbe kujerar ‘Dan majalisa mai wakiltar Mazabar Binji ya dauki wannan mataki ne daf da zaben da za ayi.

"Abin da ya sa na canza sheka (zuwa jam’iyyar PDP) shi ne ganin irin nasarorin da gwamna Aminu Tambuwal ya samu a cikin wani lokaci." Inji Lili.

“A lokacin da mu ke PDP, mun kalubalanci zabensa, kuma aka yi zaben karashe wanda ya yi nasara, mu ka kai shi kotu, aka dage shari’a, a karshe ya ci.”

KU KARANTA: Mutane sun ragargaji tsohon Sanatan PDP bayan an ga hoton gidansa

Sokoto: Hon. Bature Lili ya koma Jam’iyyar PDP mai mulki a Binji
Bature Lili ya ce alamu sun nuna Ubangiji ya na tare da Tambuwal
Asali: Twitter

“Mun kai shi kotun daukaka kara (bayan kotun zabe), ya yi nasara. Bayan ba mu gamsu ba, mu ka kai shi kotun koli, a nan ma aka sake ba shi nasara.”

“A kan menene mutum zai cigaba da fada da wanda Ubangiji ya nuna ya na goyon bayansa? A Ranar Asabar ake sa ran cewa za a sake shirya zaben yankin.

‘Dan siyasar ya fadawa Magoya bayansa cewa ya janye takarar da za a karasa a karshen makon nan na kujerar Binji da ya taba rikewa a Majalisar jihar.

A jiya wasu ‘Yan bindiga sun harbe ‘Dan Jam’iyyar APC, Tunde Oreitan a Garin Ibadan. Yanzu haka Gari ya turnuke bayan kisan wannan Jigon Jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng