An kashe kasurgumin mai garkuwa da mutane 'Yunusa Boka'

An kashe kasurgumin mai garkuwa da mutane 'Yunusa Boka'

Hukumar yan sandan jihar Katsina ta alanta hallaka Yunusa Boka, kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ya ke aika-aikansa a Danmusa da karamar hukuma Kankara ta jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya bayyana hakan ne a jawabin da saki ranar Laraba inda yace an hallaka Yunusa Boka ne a musayar wuta da yayi da jami'an tsaro a dajin Gwarzo, karamar hukumar Matazu ranar Talata.

Kakakin, Gambo Isah ya kara da cewa gamayyar jami'an yan sanda, Sojoji da tubabbun yan bindiga suka kai harin kuma sun ceto wata mata da jaririnta mai wata bakwai da haihuwa.

Yace: "Bisa ga rahoton leken asiri, an shirya gamayyar jami'an yan sanda, Sojoji da tubabbun yan bindiga domin kai farmaki mabuyar masu garkuwa da mutane a dajin Gwarzo, karamar hukumar Matazu"

"Bayan musayar wuta da yan bindigan, an samu nasarar kashe kasurgumin mai sace mutane, Yunusa Boka, wanda ya addabi al'ummar yankin."

"Hakazalika an ceto wata mata Firdausi Yusuf, yar kauyen Burunkuza da jaririnta dan watanni 7, Amin Yusuf."

DUBA NAN: Yau a tarihi: Hadarin jirgin da yayi sanadiyar mutuwar mahajjata kimanin 180 a Kano a 1973

Gambo ya ce an garzaya da matar da yaronta asibitin Danmusa domin duba lafiyarsu kuma tuni an mayar da su wajen yan'uwansu.

Ya yi kira ga mutan jihar su taimakawa jami'an tsaro da labarai kan yan tada zaune tsaye a unguwanninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel