Amotekun: Afenifere ta yi wa Tinubu martani mai zafi

Amotekun: Afenifere ta yi wa Tinubu martani mai zafi

Sakataren kungiyar Afenifere na kasa, Kole Omololu, ya caccaki jagaban Bola Tinubu a kan matsayarsa a sabon salon tsaro da aka kirkiro a yankin Kudu maso yamma mai suna Amotekun.

Idan za a tuna, a ranar Laraba ne Tinubu yayi magana da manema labarai a kan matsayarsa a kan Amotekun, kwanaki kadan bayan tsananin kalubalen da ya fuskanta don ya ki tofa albarkacin bakinsa a kai.

A wata takarda da tsohon gwamnan jihar Legas din ya fitar, ya ki sanar da matsayarsa a kan lamarin.

A yayin mayar da martani, Omololu ya zargi Tinubu da sanya siyasa a lamarin da ya shafi tsaro da hadin kan Yarabawa a yankin Kudu maso yamma.

Sakataren Afenifere din ya musanta cewa kamata yayi Tinubu ya soki matsayar ministan shari'ar kasar nan, Abubakar Malami (SAN).

Tun a farko dai Malami ya ce Amotekun bai dace da shari'a ba kuma bashi da tushe a kundin tsarin mulkin kasar nan.

DUBA WANNAN: Shugaban PDP na Kano, Rabiu Bichi ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC

A wata takarda da aka mika wa jaridar The Punch, Omololu ya ce, "Martanin Asiwaju shi muke kira da daidaituwa a siyasance. Ya kamata shugabanni su fito kiri-kiri a kan lamarin da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya." cewar sakataren.

"Asiwaju ya ki tsokaci a kan sauran hukumomin tsaron da basu kundin tsarin mulki kamarsu Hisbah da JTF na farar hula a arewa. Bai karanta takardar AGF dalla-dalla ba don a bayyane ta ke cike yake da tsoro. Tsoron cewa Amotekun zata hada kan Yarabawa ba tare da duban bangarorin siyasa ba." ya ce.

"Amotekun na da goyon bayan dukkan 'ya'yan Oduduwa da sauran 'yan kasa banda Fulani. Hadin kan na da matukar hatsari ga gwamnatin da ke duba yankin. Mun shirya jajircewa a kan kalamai dubbai irin na Tinubu saboda babu adalci a ciki." takardar ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel