Maganganu 7 da Tinubu ya yi game da ‘rundunar tsaron Yarbawa’ daya jawo cecekuce

Maganganu 7 da Tinubu ya yi game da ‘rundunar tsaron Yarbawa’ daya jawo cecekuce

Jigon jam’iyyar APC, kuma jagoran yarbawan Najeriya a siyasance, Sanata Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya yi furuci game da tirka tirkar da ta dabaibaye ‘rundunar tsaron yankin yarbawa’ da gwamnonin shiyyar kudu maso yamma suka kirkira da suna ‘Amotekun’.

Daily Trust ta ruwaito an shiga rudani a yankin yarbawa biyo bayan shirun da aka ji Tinubu yayi game da Amotekun, musamman tun bayan da gwamnatin tarayya ta haramta rundunar, wanda hakan ya sa shuwagabannin yarbawa suka dinga tofin Allah tsine a kan gwamnati, amma ba’a ji muryar Tinubu ba.

KU KARANTA: An yi ba’a yi ba: Barawo ya sulale daga Kotu a lokacin da Dansanda yake sharbar barci

Maganganu 7 da Tinubu ya yi game da ‘rundunar tsaron Yarbawa’ daya jawo cecekuce
Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnonin yankin Yarbawa sun kirkiri Amotekun ne domin ya magance tarin matsalolin tsaron da ake fama dasu a yankin su da suka hada da fashi da makami, satar mutane, garkuwa dasu, hare haren yan bindiga da sauransu.

Ga wasu daga cikin muhimman bayanan da Tinubu yayi game da rundunar;

- Tinubu ya nemi a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnonin yankin Yarbawa da ministan shari’a Abubakar Malami game da Amotekun

- A cewar Tinubu, kafa runduna kamar Amotekun ba zai kawo barazanar tsaro ga kasar Najeriya ba

- Amma ya yi kashedi ga duk masu furta munana kalamai game da Amotekun, inda yace ire iren furucin nan ne zai iya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

- Haka zalika Tinubu ya gargadi masu ganin gwamatin tarayya na yunkurin danne yankin kudu maso yamma ne, inda yace suna ruwa.

- Tinubu ya kara da cewa duk masu goyon bayan Amotekun basu da cikakken masaniya game tsarin, amma sun fi kowa zakewa wajen muzanta masu adawa da ita.

- Bugu da kari ya caccaka masu adawa da tsarin saboda a cewarsa basu san komai game da shi ba, suna adawa ne kawai saboda abokan hamayyarsu ne suka bullo da ita, ko kuma don babu abin da zasu samu a cikinta.

- Daga karshe yace Amotekun dama ce da Najeriya za ta tabbatar da tsarin mulkin Fediraliyya, amma hakan ba zai samu ba ta hanyar cin mutunci ba, sai dai ta kwanciyar hankali da tunani mai zurfi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel