A karshe: Tinubu ya yi magana a kan 'Amotekun', ya bayyana matsayarsa

A karshe: Tinubu ya yi magana a kan 'Amotekun', ya bayyana matsayarsa

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya katse shirun da ya yi a kan batun kafa hukumar tsaro ta yankin 'yan kabilar Yoruba, watau 'Amotekun'.

Batun kafa hukumar tsaro ta 'Amotekun' da gwamnonin jihohin kabilar Yoruba suka yi yana cigaba da daukan hankalin jama'a a sassan Najeriya.

Sai dai, duk cece - kucen da ake yi a kan 'Amotekun', Tinubu bai fito fili, a baya, ya bayyana matsayarsa ba, lamarin da yasa ake sukarsa a kan shirun da ya yi a kan batun da ya shafi yankinsa da kuma al'ummar kabilarsa.

A cikin jerin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Tinubu ya bayyana cewa wasu mutane ne suke ta 'gutsuri tsoma' a kan kafa hukumar 'Amotekun' saboda sun jahilci abun ko kuma don suna jin haushin cewa ba sune suka zo da tunanin ba.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatocin yankin kudu maso yamma sun kafa 'Amotekun' ne da niyyar taimakon gwamnatin tarayya a bangaren inganta tsaro amma sai wasu mutane marasa kishin kasa suka shafa wa batun 'kashin kaji' don su bata shirin.

A karshe: Tinubu ya yi magana a kan 'Amotekun', ya bayyana matsayarsa
Bola Tinubu
Asali: Facebook

A cewar Tinubu, "lamari ne da yake bukatar duba na tsanaki, da yawa daga cikin masu suka da kumfar baki a kan Amotekun, basu da ilimi a kan dokoki da kuma kundin da zai zama jagora ga aiyukan sabuwar hukumar ba. Wasu kuma suna sukar batun ne saboda basu ga ta hanyar da zasu samu kudi daga kafa hukumar ba."

DUBA WANNAN: 2023: Dattijan 'yan siyasar arewa 4 da suka cancanci samun mulkin shugaban kasa

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya cigaba da cewa, "wasu suna son yin amfani da shirun da nayi a kan batun 'Amotekun' domin su ingizani na yi magana cikin gagga wa saboda su samu kuskuren da zasu yi amfani da shi wajen suka da bata min suna."

Jagoran na jam'iyyar APC ya kara da cewa ya fara magana da shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na 'yan kabilar Yoruba domin ganin an warware duk wata sarkakiya a kan 'Amotekun' cikin sauki.

Kazalika, ya yi kira ga ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami, wanda ya soki kafa Amotekun, da ya gana da kungiyar gwamnonin jihohin kabilar Yoruba domin warware duk wata rashin fahimta ko cin karo da dokokin tarayya da kafa hukumar ya haifar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel