An nemi Uban ango da Uwar amarya an rasa, yayin da ake saura kwanaki kadan daurin aure

An nemi Uban ango da Uwar amarya an rasa, yayin da ake saura kwanaki kadan daurin aure

- Burin kasancewar wasu masoya biyu na har abada ya tsaya cak a yankin yammacin Gujarat na kasar Indiya

- Ana saura kwanaki 11 bikinsu ne aka nemi mahaifin ango da mahaifiyar amarya aka rasa

- Makusantansu sun tabbatar da cewa tsoffin masoyan juna ne kuma sun tsere ne don tabbatar da cikar burin tsohuwar soyayyarsu

Jaridar Independent.UK ta ruwaito yadda aka fasa bikin auren wasu masoya bayan mahaifin ango da mahaifiyar amarya sun bace. An zargi cewa guduwa suka yi kamar dai yadda masoyan da suke tunanin soyayyarsu bata da mafita ke yi.

Matasan daga yankin yammacin Gujarat na kasar Indiya na ta zumudin zasu kasance tare bayan daurin aurensu da za a yi a watan Fabrairu na 2020. Anyi shekara daya cif ana ta shirin bikin masoyan.

Amma kuma tuni aka tsayar da shirin auren bayan an gano cewa mahaifin ango mai shekaru 48 tare da mahaifiyar amarya mai shekaru 46 sun tsere ana saura kwanaki 11 bikin, kamar yadda jaridar The Times of India ta ruwaito.

KU KARANTA: Yadda Fasto ya tunzura budurwa za ta kashe kanta, bayan ya wallafa hotunanta tsirara a soshiyal midiya

Mahaifin angon mai sana'ar suturu ya bar gidan shi da ke yankin Katargam na birnin Surat, yayin da mahaifiyar amaryar kuwa ta bar gidanta da ke Navsari.

Dukkan iyalan sun bayyana batan iyayen nasu amma anyi zargin cewa sun gudu ne sakamakon wata tsohuwar soyayya.

Wani dan uwan iyalan ya bayyana cewa iyayen da suka bace sun san juna don a yanki daya suka taso. Hakazalika abokansu na kusa sun tabbatar da cewa tsoffin masoyan juna ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng