Rundunar soji ta yi gargadi kan tashohin bincike na bogi a titin Maiduguri-Damaturu

Rundunar soji ta yi gargadi kan tashohin bincike na bogi a titin Maiduguri-Damaturu

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya karya shirunsa a kan dawowar hare-haren yan ta’addan Boko Haram a hanyar Babbar titin Maiduguri-Damaturu, ya gargadi masu ababen kan tashoshin bincike na bogi da yan ta’addan suka kafa kan babbar titin.

Kwamandan ya ci gaba da bayanin cewa kada masu ababen hawa su tsaya a kowani tashar bincike sai wanda mahukunta suka kafa a wasu wurare a hanyar, inda ya ce tashoshin bincike sahihai sune a yankunan Benisheikh, Jakana, Auno, Mainok da Njimitilo.

Manjo Janar Adeniyi ya bayyana hakan ne a wata hira da yan jarida a cibiyar rundunar Operation lafiya dole da ke Maiduguri.

Ya bayyana dawowar hare-haren yan ta’addan kan hanyar a matsayin rashin samun damar kafa cibiyarsu a kowani yanki na Najeriya.

Ya cigaba da bayyana cewa mafi akasarin wadanda yan Boko Haram suka sace ana amfani dasu ne a matsayin bayi a harkar kamo kifi da noma.

KU KARANTA KUMA:

Kwamandan ya ce daga yanzu yan ta’addan Za su dandana kudarsu a hannun rundunar sojin Najeriya idan suka cigaba da kai hare-hare a hanyar Maiduguri-Damaturu, cewa sojoji na aiki ta hanyar don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel