Kaico: Yan bindiga sun yi awon gaba da diyar wani jigon APC a Filato

Kaico: Yan bindiga sun yi awon gaba da diyar wani jigon APC a Filato

A ranar talata ne wasu 'yan bindiga suka sace diyar tsohon kwamishinan jihar Filato, Peter Mwadkon. Christe Peter diyar jigon jam'iyyar APC ce wacce aka yi awon gaba da ita wajen karfe 2 na dare a gidan yayarta da ke yankin Kwata da ke karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Filato.

Jaridar The Nation ta gano cewa 'yan bindigar sun shiga gidan ne inda suka dauka wani yaro amma sai suka dawo don aje shi tare da daukar Christe wacce ta kammala digirinta a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

An ji masu garkuwa da mutanen na musu tsakaninsu bayan sun sace yaron mai shekara 10. Suna musun cewa budurwa aka aiko su don dauka ba yaro ba.

A halin yanzu dai masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan tsohon kwamishinan inda suka bukaci har naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon Alƙalin kotun kolin Najeriya rasuwa

Garkuwa da budurwar ya biyo baya ne sa'o'i 6 bayan an kashe wani Gabriel Bulus mai shekaru 27 a kauyen Torok dake yankin Rim na karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato.

An kashe Bulus ne da misalin karfe 8 na yamma a ranar Litinin bayan hararsu da wasu da ake zargin makiyaya suka yi.

Rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da aukuwar lamurran kuma sun tabbatar wa da iyalan wadanda abin ya faru dasu cewa za a zakulo wadanda ake zargi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Terna Tyopev ya tabbatar wa da jaridar The Nation aukuwar lamarin a wayar tarho. Ya ce Bulus na dawowa ne daga karbo cajin wayarsa inda ya gamu da ajalinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel