2023: Dattijan 'yan siyasar arewa 4 da suka cancanci samun mulkin shugaban kasa

2023: Dattijan 'yan siyasar arewa 4 da suka cancanci samun mulkin shugaban kasa

Najeriya kasa ce mai cike da albarkatu tare da mutane masu tsantsar baiwa. Akwai 'yan siyasa masu tsananin gogewa da sanin abinda suke yi a siyasance. Ganin karatowar 2023 kuma shugaba Buhari ba zai sake tsayawa takara ba, ana ta hasashen gogaggun 'yan siyasar Najeriya da zasu dace da kujerar da shugaban kasar zai bari.

1. Sule Lamido

Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa ne wanda ya taba zama a gidan kaso an wani lokaci. An sako shi kuma har yanzu ana shari'arsa da wasu yaransa biyu tun daga 2015 a kan almundahanar kudaden jihar. Ya mulki jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015. Tsohon ministan al'amuran waje ne daga 1999 zuwa 2003.

2. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kokarin bige Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Ana matukar tsammanin cewa zai fito takar a 2023. Shi ne babban dan adawa don kuwa ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP wanda hakan yasa ya samu tikitin takara a karkashin jam'iyyar a zaben 2019.

DUBA WANNAN: Buhari ya sabunta nadin mutane 2 dake bashi shawara a kan lamuran gajiyayyu

3. Bukola Saraki

Olubukola Abubakar Saraki an haifesa ne a ranar 19 ga watan Disamba 1962. Kwararren likita kuma dan siyasa ne. Shi ne tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya karo na takwas kuma tsohon gwamnan jihar Kwara a karkashin jam'iyyar PDP. Ya fadi zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a 2019 ga Atiku Abubakar.

4. Rabiu Musa Kwankwaso

Injiniya Rabiu Musa wanda aka fi sani da Rabiu Kwankwaso kwararren dan siyasar Najeriya ne daga jihar Kano. Ya yi shugabancin jihar har sau biyu. SHi ne gwamnan na farko a jihar da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP a jamhuriya ta hudu. Duk da ya fito takarar shugabancin kasa a 2019, Atiku Abubakar ya kada shi a zaben fidda gwani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel