Ka zo mu hada hannu mu gyara barnarka – Bala Muhammad ga tsohon gwamnan Bauchi

Ka zo mu hada hannu mu gyara barnarka – Bala Muhammad ga tsohon gwamnan Bauchi

- Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya yi kira ga tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abubakar, da ya zo su hada hannu da gwamnatinsa domin kawo cigaba a jihar

- Bala Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja bayan tabbatar da nasarar zabensa da Kotun koli ta yi

- Muhammad Abubakar ya kasance babban abokin adawarsa a zaben gwamnan 2019

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya yi kira ga tsohon gwamnan jihar kuma abokin karawarsa a zaben gwamnan 2019, Muhammad Abubakar, da ya zo su hada hannu da gwamnatinsa domin kawo cigaba a jihar.

A cikin wata sanarwa daga babban hadimin gwamnan a kafofin watsa labarai, Muktar Gidado, ya bayyana cewar gwamna Bala Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja bayan tabbatar da nasarar zabensa da Kotun koli ta yi a jiya Litinin, 20 ga Janairu.

Gwamnan ya bayyana cewar hada karfi da karfe wuri gudan, zai baiwa gwamnatinsa zarafi da damar shawo kan dumbin matsalolin da jihar ke fuskanta da kuma tabbatar da kyautata jihar Bauchi zuwa ga mataki na gaba.

Ya ce: “Na mika hannayena don mu yi musabaha da abokin hamayya na kuma dan takarar APC da na kayar, Muhammad Abubakar ne domin mu tabbatar da aiwatar a ayyukan da shi ya gaza yin su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Da karfe 2 na rana Kotun koli za ta yanke hukunci kan zabukan gwamnan Adamawa da Benue

“Nasarata da kotun koli ta tabbatar, yana kara tabbatar da inganci tsarin shari’a a kasar nan, ina son na tabbatar wa al’umman jihar Bauchi da suka amince suka zabeni, cewa zan tabbatar da yin gwamnatina ba tare da nuna wariya ko banbanci ba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng