EFCC: Wasu wadanda ake zargi da laifi sun shiga hannu a Jihar Oyo

EFCC: Wasu wadanda ake zargi da laifi sun shiga hannu a Jihar Oyo

Jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, sun yi wani kamu a jihar Oyo inda su ka damke mutane da-dama.

Kamar yadda mu ka samu labari daga gidan talabijin na Channels TV, mutane akalla 89 Dakarun EFCC su ka kama a wani gidan rawa da ke Garin Ibadan.

An kama wadannan mutane ne a wani fitaccen gidan rawa a Garin mai suna 360, ana zarginsu da laifin damfarar jama’a da zamba ta kafafen yanar gizo.

Ma’aikatan hukumar EFCC sun yi nasarar cafke wadannan mutane ne bayan sun dauki lokaci su na bibiyar sawunsu kamar yadda su ka bayyana mana.

EFCC ta shaidawa ‘Yan jarida cewa sun yi wannan kame ne a karshen makon da ya wuce. Bisa dukkan alamu an kama mutanen ne a Ranar Lahadi.

KU KARANTA: Duk da karin VAT, Najeriya ta fi kowace kasa a Afrika saukin haraji

EFCC: Wasu wadanda ake zargi da laifi sun shiga hannu a Jihar Oyo
EFCC ta kama wasu da ake zargi da damfara a gidan rawa
Asali: Depositphotos

Labarin wannan samame da jami’an kasar su ka kai wa wadanda ake zargi da laifin ya zo wa Manema labarai ne a jiya Ranar 20 ga Watan Junairu, 2020.

Ana zargin wannan gidan rawa da ke kan babban titin Alao Akala a Garin Ibadan da zama wajen shakatawan hatsabiban ‘Yan damfara da ke Yankin.

Rundunar EFCC ta reshen jihar Oyo ne su ka dauki alhakin wannan kame da aka yi. Ana yi wa wadannan ‘Yan damfara lakabi da “‘Yan Yahoo-Yahoo.”

Da zarar jami’an EFCC sun kammala bincikensu, za su mika wadannan mutane da ake zargi da laifi gaban kotu domin a yanke masu hukuncin da ya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel