Kotun koli: Gwamnan Jihar Ribas ya aikawa Tambuwal sakon murna

Kotun koli: Gwamnan Jihar Ribas ya aikawa Tambuwal sakon murna

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya taya Takwaransa na jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal murnar samun nasara a kotu.

Mai girma gwamna Nyesom Wike ya aika wannan sako ne jim kadan bayan kotun koli ta ba gwamnan gaskiya a shari’ar zaben 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa Wike ya aika wannan sakon barka ne ta bakin Kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Polinious Nsirim.

A jawabin da aka fitar, gwamnan ya ce hukuncin da Alkalan kotun koli su ka yi, ya tabbatar da goyon bayan da jama’a su ka ba Tambuwal.

“Ina kira ga gwamna (Aminu Waziri) Tambuwal ya yi aiki domin hadin kai da cigaban jihar Sokoto, ta hanyar aiki da kowa.” Inji sa.

KU KARANTA: Gwamnatin Wike ta ruguza Masallacin Juma'a a Jihar Ribas

Kotun koli: Gwamnan Jihar Ribas ya aikawa Tambuwal sakon murna
Gwamn Wike ya ce aikin Kotun koli ya yi kyau a shari'ar Sokoto
Asali: Depositphotos

Bayan shawarar kafa gwamnatin gammayya domin kawowa Sokoto cigaba, Nyesom Wike ya yabawa Alkalan kotun kolin kasar.

Nyesom Wike ya jinjinawa babbar kotun Najeriyar da ta yi kokari wajen ganin sun ba zabin al’umma gaskiya a shari’ar da aka yi.

Kwanakin baya Mista Wike ya aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari irin wannan sakon murna bayan da ya doke PDP a kotu.

Akwai alamun da ke nuna gwamnonin biyu sun shaku, har Wike ya marawa Tambuwal baya wajen samun tutar PDP a zaben 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng