Hukuncin kotun koli: Buhari ya taya gwamnonin jam’iyyar APC guda 2 murna

Hukuncin kotun koli: Buhari ya taya gwamnonin jam’iyyar APC guda 2 murna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamnonin jam’iyyar APC guda biyu murnar nasarar da suka samu a gaban kotun koli game da tirka tirkan shari’ar zaben su da suka yi ta fama da shi.

Wadannan gwamnoni guda biyu yan gatan jam’iyyar APC sun hada da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jahar Filati Simon Lalong. Sai dai shugaban kasa ya yi gum game da nasarar gwamnonin PDP da suka hada da Tambuwal da Bala Muhammad, inji rahoton Punch.

KU KARANTA: El-Rufai ya kaddamar da ilimi kyauta a Kaduna daga Firamari har zuwa Sakandari

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, inda ya taya jam’iyyar APC murana bisa nasarar da ta samu a jahohin Kano da Filato.

“Ina farin cikin kawo karshen wannan tirka tirka da kuka yi ta fama da shi, tare da nasarar da jam’iyyarmu ta samu da kuma gwamnoninmu. APC ce ta ji jahohin nan, kuma ta tabbatar ma kotu da haka, da ya zama babban asara a garemu idan da mun rasa jahohin Filato da Kano saboda muhimmancinsu.

“Ya zama wani sabon yayi ga yan siyasa su shigar da karar duk wani zabe ko hukunci da bai musu dadi ba. A wurinsu zabe yayi kyayu idan sun samu nasara, amma idan basu samu ba bai yi kyau ba, amma su sani ba haka siyasa take ba.” Inji shi.

Daga karshe shugaba Buhari ya kira ga dukkanin yan siyasa da mabiyansu dasu cigaba da karfafa tsarin dimukradiyya da kuma tsarin sharia ta hanyar neman warware duk wasu matsaloli a gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel