Damfarar N111m: Kotu ta garkame 'Mama Boko Haram' a kurkuku

Damfarar N111m: Kotu ta garkame 'Mama Boko Haram' a kurkuku

Wata babbar kotun jihar dake zamanta a Maiduguri, birnin jihar Borno, ta bada umurnin garkame Aisha Wakil wacce aka fi sani da 'Mama Boko Haram, a gidan gyara hali a ranar Litinin, 20 ga Junairiu, 2020.

Alkali mai shari'a, Aisha Kumaila, ta bada umurnin ne yayinda hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Aisha Wakil tare da Tahir Saidu Daura da Lawal Shoyade, kan zargin damfara na kimanin milyan goma sha daya (N111, 650,000.)

EFCC ta ce a shekarar 2018, Mama Boko Haram da abokan laifinta sun yaudari wani Mohammed Umar Mohammed, ta hanyar amsan kwangilan gyara Chison 600A (na'urar hoto a asibiti), sifiku da kuma odar wake ta kungiyarsu (Complete Care and Aid Foundation).

Aisha da abokan laifinta sun musanta zargin da EFCC ke musu.

Bayan haka lauyan EFCC, Benjamin Manji, ya bukaci kotun ta wani ranar gurfanar da su kuma a garkamesy a gidan yari kafin a gama sauraron karar.

Alkalin ta bada umurnin ajiyesu a gidan gyara hali kuma ta dage karar zuwa ranar 10 ga Febrairu 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel