Mutane 17 sun mutu, 14 sun samu rauni a mummunan hatsari a Katsina

Mutane 17 sun mutu, 14 sun samu rauni a mummunan hatsari a Katsina

Da yammacin ranar Litinin ne rahotanni suka bayyana cewa an samu afkuwar wani mummunan hatsarin mota da wata babbar motar daukan kaya (Tirela) ta haddasa a kauyen Yardudu dake kan hanyar zuwa Shargalle a yankin karamar hukumar Mashi, jihar Katsina.

Rahotannin sun bayyana cewa hatsarin motar ya yi sanadiyyar mutane 17 tare da raunata wasu mutane 14.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, da aka raba wa manema labarai, rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa wani nai suna Sale Hangay, mai shekaru 35 daga Katsina, shine direban babbar motar data yi hatsarin.

A cewarsa, "hatsarin ya afku ne bayan kan babbar motar ya fita daga gangar jikinta sannan ya fada kasan wata gada. Motar, wacce ta taso daga karamar Mai'addu'a, tana dauke da shanu da za a kai jihar Legas.

"An garzaya da dukkan wadanda hatsarin ya ritsa da su zuwa karamin asibitin garin Mashi domin a ceto rayuwarsu. Likitoci sun tabbatar da mutuwar 17, yayin da wasu mutanen 14 suka samu munanan raunuka,"a cewarsa.

Jawbin ya kara da cewa kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Sanusi Buba, yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu da kuma sauran al'ummar jihar Katsina tare da kiran taron gagga wa da shugabannin kungiyar direbobi da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufuri a jihar Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng