Yanzu yanzu: PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja

Yanzu yanzu: PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara zanga-zangar da ta shirya a Abuja a safiyar ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da wasu manyan mambobinta na daga cikin mutanen da suka halarci gagarumin zanga-zangar wanda ke gudana a yanzu haka.

Babbar jam’iyyar adawar a wani jawabi da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ya zama dole kotun koli ta janye hukuncinta kan zaben gwamnan jihar Imo wanda ya sallami dan takararta, Emeka Ihedioha, sannan ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hope Uzodinma a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar.

Yanzu yanzu: PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
Asali: UGC

Yanzu yanzu: PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
Asali: UGC

Yanzu yanzu: PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
PDP ta fara gagarumin zanga-zanga a Abuja
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Zabukan gwamna: An janye Shugaban alkalan Najeriya daga kwamitin kotun koli

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Justis Sylvester Ngwuta ne ya jagoranci kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar.

Sauran mambobin sun hada dan Justis Kudirat Kekekere-Ekun, Justis Olukayode Ariwoola, Justis Amina Augie da kuma Justis Uwani Abba-Aji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng