Yadda na boye cikin Daji daga masu garkuwa da mutane – Mai martaba Baburam

Yadda na boye cikin Daji daga masu garkuwa da mutane – Mai martaba Baburam

Mai martaba Sarkin kasar Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, ya bada labarin yadda ya samu kansa a tsakiyar masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Alhaji Umaru Bubaram ya bada wannan labari ne a wata hira da aka yi da shi a Jaridar Daily Trust kamar yadda aka wallafa a jiya Ranar Lahadi, 19 ga Watan Junairu, 2020.

“Abin dai ya faru ne daf da Garin Jaja, kafin Mararrabar Jos. Mu na cikin tafiya sai mu ka fahimci akwai matsala a kan titin. Saboda haka mu ka dakata, kafin nan mu ka cigaba.”

“Bayan kusan minti 20 sai hanya ta bude, motoci su ka fara tafiya. An yi rade-radin cewa Miyagu sun tare hanyar ne, amma daga baya aka sa kai, ni dai ina ganin akwai hadari.”

“Kusan kilomita hudu da tafiya kenan sai hanya ta kara cabewa, bayan ‘yan mintuna aka fara harba bindigogi ta dama da hagu, abin ba a magana, kamar ana wajen yaki.”

KU KARANTA: An gano wadanda su ka kai wa Sarki hari har aka kashe Dogarai

Yadda na boye cikin Daji daga masu garkuwa da mutane – Mai martaba Baburam
Umaru Baburam ya rasa wasu Dogarai hudu a harin Miyagu a Kaduna
Asali: Twitter

“Daga nan na ga Direbana ya juya, ya buge wata mota, na dauka an harbe sa ne, na fahimci abin ya yi kamari. Sai kuma na ga ‘Dan Sanda na ya na kokarin fitowa daga mota.”

“A nan mu ka fito mu ka rabu da motocinmu, domin mu tsira da ranmu. Ubangiji da rahamarsa, ya cece mu, mu ka tsere daga wajen harin. Mu ka ci tafiya kafin mu tsaya.”

“Mu ka yi ta faman tafiya, mu ka dakata, mu ka cigaba har mu ka tabbatar mun kaucewa hadarin. Mu ka fake cikin daji. Wajen 2:00 na dare, na hangi hasken fitilar nema na.”

“Na ce bai kamata in fito a cikin daren nan ba, na kuma guji taba waya ta har sai bayan an kira Sallar asuba, hanya ta washe. Da safe, ‘Yan Sanda su ka kira, su ka dauko ni.”

Daga nan ne aka wuce da shi zuwa asibiti. Sarkin ya godewa irin kokarin da Minista Abubakar Aliyu da Kakakin jihar Yobe da Gwamnatin Kaduna su ka yi masa bayan harin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel