2019: Sanata Ifeanyi Ubah ya tafi gaban kotun daukaka kara - Hadiminsa

2019: Sanata Ifeanyi Ubah ya tafi gaban kotun daukaka kara - Hadiminsa

Sanata Ifeanyi Ubah ya soki hukuncin babban kotun tarayya na tsige shi da kan kujerar Sanata mai wakiltar Mazabar Anambra ta Kudu a majalisar dattawa.

Kamar yadda mu ka samu labari, Ifeanyi Ubah ya bayyana cewa tuni har ya sheka gaban kotu na gaba, ya daukaka kara ta hannuna Lauyoyin da ke karesa.

Sanatan ya bayyana cewa ba ayi masa adalci a kotun tarayya na Kubwa ba, domin ba a saurari duk korafin da Lauyoyinsa su ka gabatar a gaban Alkali ba.

Kotun tarayya ba ta hurumin sauraron abin da ya faru bayan zabe. ‘Dan majalisar ya fadi wannan jawabi ne ta bakin wani Hadiminsa, Adichie Izuchukwu.

KU KARANTA: Kotu ta tabbatar da karbe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu

2019: Sanata Ifeanyi Ubah ya tafi gaban kotun daukaka kara - Hadiminsa
Ifeanyi Ubah ya ce bai yarda da hukuncin kotun tarayya ba
Asali: Depositphotos

Adichie Izuchukwu ya ce kotun sauraron korafin zabe ne kurum ke da ikon yanke hukuncin game da abin da ya auku bayan zabe, ba wai kotun tarayya ba.

“Kotu ba ta hana Ubah damar kare kansa, ta hanyar kin waiwayar bukatun da Lauyoyinsa su ka kawo. Sai dai aka ce kwanaki 180 na sauraron karar abubuwan da su ka faru kafin zabe ya wuce.”

“Haka Kotu ba ta yi la’akari da irin shari’ar da aka yi tsakanin Uche Nwosu da jam’iyyar AA a Kotun koli inda Alkalai su ka ce shudewar lokaci ba zai shafi zaben da ba a yarda da shi ba.”

“Kuma Kotu ba ta saurari korafinmu na cewa karar da Lauyan Obinna Uzoh ya shigar, ya zo ne bayan zabe, don haka batu ne na bayan zabe wanda maganar kwanaki 180 ba za su yi aiki ba.”

A karshe ‘Dan majalisar Datttawan ta bakin Hadimin na sa, ya yi kira ga Magoya bayansa su kwantar da hankalinsu domin ya na sa ran gaskiya a kotun gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel