Imo: Yadda kotun koli ta dumbuzawa Hope Uzodinma kuri’u - YIAGA

Imo: Yadda kotun koli ta dumbuzawa Hope Uzodinma kuri’u - YIAGA

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar YIAGA Afrika ta yi magana a game da shari’ar zaben jihar Imo, inda ta ce Alkalan kotun koli sun ba jam’iyyar APC kyautar tarin kuri’u.

Wannan kungiya ta ce kotun koli ta ba Sanata Hope Uzodinma kuri’u 92, 597 da ba na shi ba a lokacin da ta tsige gwamna Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP daga kan kujerar.

“Kotun koli ta dogara ne da kuri’un da aka samu a Mazabu fiye da 300 wanda INEC ta ki lissafi da su saboda an sabawa doka na rashin amfani da na’urar tantance kuri’u da tada hayaniya.”

“Ya za ayi ace jam’iyyu biyu kacal aka samu da kuri’u a cikin Mazabu fiye da 366 a zaben da ‘Yan takara 70 za su ka fito” Inji Darektan kungiyar YIAGA Afrika watau Mista Samson Itodo.

Wannan shi ne sakamakon zaben da aka samu kafin a shiga kotun koli:

Yawan rumfunan zabe = 3, 523

Adadin wadanda aka tantance = 823,743

Adadin kuri’u masu kyau da aka kada = 714,355

Adadin kuri’un da aka soke = 25,130

Ainihin gaba daya kuri’un da aka kada = 739,485.

KU KARANTA: Ana zanga-zanga saboda hukuncin da aka yi a zaben Gwamnan Imo

“Banbancin Masu kada kuri’un da aka tantance da ainihin kuri’un da aka kada shi ne 84,258. Wannan idan an hada har da kuri’un da aka soke saboda ba ayi amfani da na’ura ba.”

“A lissafin INEC, tazarar APC da PDP shi ne kuri’a 176,946. A hukuncin kotun koli, an fahimci cewa ‘Dan takarar APC ya samu fiye da kuri’a 176,969 a Mazabun nan 366 da aka soke.”

“Idan mu ka yi aiki da kuri’un 176,969 kafin kotun koli ta fitar da hukunci; Kuri’u 176,969 a tara da 739, 485 (Yawan kuri’un da aka kada), za a samu 916,431 wanda ya zarce masu zabe.”

“Ainihin adadin wadanda aka tantance su kada kuri’a su ne mutum 823,834.” Itodo ya ce: “Daga ina aka samo ragowar kuri’a 92,597?” Itodo ya ce Alkalai sun kafa mummunan tarihi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel