Tirkashi: EFCC ta bayyana wata gagarumar shaida a kan zargin da ta ke wa Shehu Sani

Tirkashi: EFCC ta bayyana wata gagarumar shaida a kan zargin da ta ke wa Shehu Sani

- An bayyana faifan murya wanda ake zargin an dauka ne yayin da yake karbar rashawa

- Tsohon Sanatan ya aminta cewa muryarsa ce amma kuma yace an sauya abin da ya fadi

- An gano cewa ya amince da zargin da ake masa bayan da yaji faifan muryar tashi

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta ruwaito cewa ta samu faifan sautin muryar da ya zama shaidarta a kan zargin da take wa tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa faifan muryoyin wadanda sun kai har 13 suna kunshe ne da hirar Shehu Sani da Sani Dauda mamallakin ASD Motors.

Hukumar yaki da rashawar ta bayyana faifan muryar ga tsohon sanatan a gaban lauyoyinsa Audu Mohammed Lawal da Glory Peter a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu. Tsohon Sanatan ya tabbatar da cewa muryarsa ce a faifan hirar amma ya zargi cewa an goge wasu sassan hirar.

Duk da Shehu sani bai zargi EFCC din da goge wasu sassa na hirar ba, ya jaddada cewa an goge wani sassa na hirar don ba cikakkiya bace.

DUBA WANNAN: Yadda aka damfareni N68.9m - Tsohon minista

Mai rajin kare hakkin dan Adam din wanda ya koma dan siyasa, ya bayyana a hirar ne yana rokon Sani Dauda da ya rufe wannan zancen gudun tozarci gaban jama'a idan ta fasu.

A wani sashi na hirar, ya tabbatar da cewa makuden kudin har $25,000 kudin cin hanci ne. Jaridar The National Daily ta bayyana cewa mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade yace za a gurfanar da tsohon sanatan a gaban kuliya.

Orilade yace: "Ana bincikar Shehu Sani kuma za a gurfanar dashi a gaban kotu."

Wannan rahoton ya ci karo da matsayar Sanatan inda ya bayyana cewa yana zargin EFCC da hada baki da Sani Dauda don bata masa suna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel