Trump ya dauko hayar manyan lauyoyi da za su hana a tsige shi

Trump ya dauko hayar manyan lauyoyi da za su hana a tsige shi

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dau kwararrun lauyoyin da zasu kare shi a gaban majalisa

- Sanannu kuma kwararrun lauyoyin sun hada da Ken Starr, Robert Ray da Alan Dershowitz

- Daya daga cikin lauyoyin yace dole ne suyi kokari saboda ana son tsige Trump ne saboda siyasa wanda hakan zai bude kofar cimma manufa ga 'yan siyasar

Donald Trump shugaban kasar Amurka ya dau kwararrun lauyoyi da zasu kare shi a gaban majalisar dattijan kasar.

Ken Starr da Robert Ray da suka yi shari'ar tsohon shugaba Bill Clinton da kuma Alan Dershowitz da ya kare dan jaridar da aka zarga da kashe matar shi a shekarar 1995 OJ Simpson na daga cikin masu kare Trump.

Fadar White House ta sanar da cewa babban lauyan Trump, Pat Cipollone ne zaiyi jagorancin tawagar. A mako mai zuwa ne za a fara sauraren karar a sabon zaman da za a gudanar.

Masana sun ce lauyoyin da zasu wakilci shugaban kasar sun shahara sosai musamman Mista Starr wanda ya gudanar da bincike a zamanin da aka zargi Bill Clinton da alaka da Monica Lewinsky, wata matashiya da ke sanin makamar aiki a fadar White House a lokacin mulkinsa.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Wani mutumi ya mutu a daidai lokacin da yake lalata da budurwa a otel

Ken Starr da Robert Ray ne su ka yi shari'ar tsohon shugaba Bill Clinton, binciken da yasa majalisar wakilai ta tsige Clinton a shekarar 1998 amma daga baya sai majalisar dattawa ta wanke shi.

A hirar shi da gidan talabijin na CBS, daya daga cikin lauyoyin, Alan Dershowitsmz ya ce shi ba dan siyasa bane, aikin da zai yi ba shi da alaka da siyasa.

A cewarshi, abune da ya shafi kundin tsarin mulki kuma yana da natsuwa kan aikin da zai yi. Yace akwai damuwa ta yadda ake son amfani da siyasa wajen tsige Trump wanda hakan zai budewa 'yan siyasa masu son zuciya kofar cimma burinsu.

Lauyan ya ce ko a baya bai aminta da tsige Clinton ba kuma Hillary Clinton ya jefa wa kuri'a a zaben 2016.

Amma kuma majiya daga fadar White House ta ce an samu rabuwar kai a kan saka sunan shahararren lauyan a cikin tawagar da za ta kare Trump, ganin alakarsa da wasu da basu ga maciji da fadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel