Nesa ta zo kusa: Nnamdi Kanu zai shigo Najeriya jana'izar iyayensa wata mai zuwa

Nesa ta zo kusa: Nnamdi Kanu zai shigo Najeriya jana'izar iyayensa wata mai zuwa

- Shugaban IPOB ya sanar da cewa zai halarci bikin birne iyayenshi da za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu

- Kanu ya bayyana cewa sun boye shirye-shiryen birnewar ne saboda idon makiya masu son tada zaune tsaye

- Kanu ya kara jaddada cewa babu gudu ba ja da baya, kafa jamhuriyar Biafra zata tabbata cikin lumana da salama

Shugaban IPOB ya sanar da cewa zai halarci birne iyayenshi da za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu na wannan shekarar.

Kanu, wanda yayi maganar ta bakin kakakin IPOB, Emma Powerful yace za a birne su ne kamar yadda al'adar yankin ta tanadar.

Ya ki sanar da shirye-shiryen birnewar da ake yi a halin yanzu saboda yanayin tsaro na kasar nan da ya duba.

Ya ce, "Za a birne iyayen shugabanmu a ranar 14 ga watan Fabrairu 2020. Ba zamu sanar da shirye-shiryenmu ba saboda akwai makiya masu fatan tarwatsa kokarinmu na ganin an birne su cike da nasara.

KU KARANTA: Budurwa ta kashe makwabcinta ta hanyar caka masa kwalba saboda ya kama mata kugu

"IPOB na nan daram kuma babu abinda zai sauya mana tunaninmu na kare muhallinmu."

Kanu ya kara jaddada cewa kungiyar na nan tana kokarin samun jamhuriyar Biafra cikin lumana da zaman lafiya.

"Kungiya ce mai cike da zaman lafiya kuma ba zamu hakura ba. Amma kuma kada wanda yace zai gwadamu," ya jaddada.

Shugaban IPOB din yayi rashin mahaifin shi mai suna Eze Israel Kanu a watanni hudu bayan mutuwar mahaifiyar shi mai suna Ugoeze Sally Kanu.

Eze Kanu basaraken gargajiya ne mai wakiltar jama'ar Afara Ukwu Umuahia har zuwa lokacin da ya mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel